You are here: HomeAfricaBBC2023 07 29Article 1814726

BBC Hausa of Saturday, 29 July 2023

Source: BBC

Ban so Henderson ya bar Liverpool ba in ji Kloop

Klopp da Henderson Klopp da Henderson

Jurgen Klopp ya ce ya so a ce Jordan Henderson ya ci gaba da taka leda a Liverpool, amma bai isa ya hana shi komawa buga gasar Saudi Arabia ba.

Tsohon kyaftin ɗin Liverpool, ya koma Al-Ettifaq, mai buga gasar Saudiyya ranar Alhamis kan fam miliyan 12.

Kloop ya amsa tambayoyin da aka yi masa kan Henderson a ganawa da 'yan jarida a lokacin da kungiyar ke wasannin atisayen tunkarar kakar bana a Singapore.

''Da ya ce yana son barin kungiyar bai kamata mu watsa kasa a garinsa ba,'' in ji Kloop.

''Hendo ya san yadda lamarin yake - cewar mun so ya ci gaba da taka leda a kungiyar, mun kuma martaba shi da yadda da hukuncin da ya yanke.''

An bai wa Henderson kyaftin ɗin Liverpool a 2015 karkashin koci Brendan Rodgers, bayan da Steven Rodgers ya bar kungiyar.

Ya ja ragamar kungiyar ta lashe Champions League a 2019 da Uefa Super Cup da Fifa Club World Cup kaka ɗaya tsakani.

Shi ne kyaftin ɗin Liverpool da ta ɗauki Premier League a 2019-20, bayan shekara 30 rabonta da shi.

Wasu kofunan da Henderson ya ɗauka a Liverpool sun haɗa da FA Cup a 2022 da League Cup a 2012 da kuma 2022.