You are here: HomeAfricaBBC2023 07 21Article 1809545

BBC Hausa of Friday, 21 July 2023

Source: BBC

'Babu mu babu Sulhu da 'yan fashi a Zamfara'

Honarabil Hamisu A Faru Honarabil Hamisu A Faru

Wasu daga cikin 'yan Majalisar jiha a Zamfara sun ce babu wani dalili da zai sa su yi sulhu da 'yan fashi a jihar.

Cikin wata tattaunawa da ya yi da BBC Honarabil Hamisu A Faru mai wakiltar mazabar Bukkuyum ta kudu a majalisar dokokin jihar ya ce "babu yadda za a yi sulhu da mutumin da bai san Allah ba".

Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan da 'yan bindigar suka kori mazauna wani kauye gaba ɗayansu a cikin ɗaya daga ƙananan hukumomin da yake wakilta kana suka mayar da shi sansaninsu.

Dan Majalisar ya ce "Gwamnan jihar ya fito ya ƙalubalanci duk wani mai neman a yi sulhu da 'yan fashin" wanda hakan ne ya ƙara musu ƙarfin gwiwa a wannan tafiya.

Ya ce akwai firgici a halin da ake ciki a jihar yanzu, domin ɓarayin sun tsallaka titin Gurusu sun bi Barayar zaki sun tsallaka Gulbi sun je wani ƙauyen Rafin Gero da ake ce masa Gyaɗo sun yi sansani, yau tsawon kwana goma kenan.

Ya kara da cewa ƙalubalen da ake fuskanta a yanzu shi ne an shiga damuna, lokacin da yaƙi da waɗannan mutane ke ƙara tsananta.

Da yawan dazuka itatuwansu sun yi kore sun zama duhuwa, tsakaninka da mutane ba tazara mai yawa amma duhu ba zai barku kuga juna ba.

"Shekaran jiya sun shiga kauyukan Ruwan rana da Yashi sun ƙona shaguna da kuma dukiya mai yawa," in ji Hamisu A Faru.

Abin da ya sa kullum ana kashe su, amma suna dawowa

An tambayi Hamisu Faru shi ko me yasa kullum ana samun rahoton an kashe mutanen nan amma sai kaga kamar ba a yaƙarsu? sai ya ce suna da yawan suna da daba kala-kala.

"Akwai dabar da ake cewa Dabar Katsalle a Kawo, ita ce ta shiga 'yar jiji da ta tsallaka Gwashi har Kyarab Zugu da Bagega, matuƙar ba a tashi wannan dajin ba tsakani da Allah ba za a samu sauƙi ba.

"Kamata ya yi idan za a yi wannan aiki a yi shi lokaci guda da na sauran jihohi da ke makwabtaka kuma suke fuskantar irin wannan tashin hankali, in ba haka ba abin ba zai ƙare ba gaskiya.

"Saboda sun yi ƙarfi gaskiya daba-daba ke da akwai, kuma kowacce daba da kwamandanta, sai an jajirce kan wannan rikici, to wannan jajircewarce gwamna ke buƙatar a yi yanzu," in Dan Majalisar.

Dalilin da ya sa suke sansani a yankunan yammaci da kudancin Zamfara

A cewar wannan Ɗan Majalisa da ɗan gari akan ci gari, akwai 'yan yankunan yammaci da kudanci a cikin wannan ta'asa da ke faruwa.

Su ne suke gayyato mutanen waje yankunan, waɗanda ke cike da duhuwar dazuka masu haɗari.

"Waɗannan dazuka su ne suka tiƙe har Birnin Gwari. Albarkatun ƙasa da ake da su shi ma wata hujja ce ta tarewar 'yan fashin dajin nan a wannan yanki.

"To waɗannan suke zama a wannan waje gashi yanzu ba sa barin mutane su yi noma, ba sa barin kowa ya yi kasuwancinsa yadda ya kamata," in ji Honarabil Faru.

"Rokon da muke ga Shugaban Najeriya da ya taimaka mana wajen murƙushe waɗannan mutane, wanda hakan zai yi daidai da burin sabon Gwamnan Jihar Zamfara."