You are here: HomeAfricaBBC2023 09 05Article 1838636

BBC Hausa of Tuesday, 5 September 2023

Source: BBC

'Babu abinci a Jibiya kuma kasuwancin mu ya durkushe saboda Nijar'

Tutar Nijar Tutar Nijar

Tun bayan umarnin da Kungiyar ECOWAS ta bayar ga kasashen da suke makwabtaka da Jamhuriyar Nijar na su rufe iyakokinsu da kasar sakamakon juyin mulki, da dama daga cikin garuruwan da suke kusa da iyakokin na kokawa dangane da yanayin matsi da suka tsinci kan su a ciki.

Garin Jibiya da ke jihar Katsina na daga cikin irin waɗannan yankuna da suke fuskantar kalubale a ɓangaren kasuwanci.

Al'ummar yankin dai sun zargi Hukumar Kwastam da hana su shigar da kayan abinci duk da cewar ba a kan iyaka suke ba.

Wasu daga cikin mazauna yankin sun shaidawa BBC cewar a halin yanzu abinci na yi musu wahala kamar yadda wani magidanci ya bayyana.

''Ko ruwa mutum ya siyo daga Katsina zai shigo Jibiya to jami'an Kwastam za su hana shi wucewa da shi, haka ma idan daga Batsari mutum ya dauko kaya zuwa Jibiya nan ma ba zai wuce da shi ba haka abun ya ke ko da daga Zamfara aka dauko kaya.

Sun ce an rufe iyaka, ko da karamar mota ce idan ku ka zo inda Kwastam suke za su duba ko karamin buhun gero suka gani ba za su bari a shiga da shi Jibiya ba''.

Mazauna Jibiya na amfani da hanyar Batsari wajen shigar da abinci domin iyalansu, hanyar kuma bata da kyau sakamakon 'yan fashin daji da ke fitowa su kona motoci.

Wani ɗan kasuwa ya bayyana takaicinsa game da motar abokinsa dauke da kayan abinci da aka kona a hanyar.

''Mun kasa gane inda matsalar take domin muna gani ana siyan kayan abinci ana shiga da su Nijar, muna shigowa da motar masara biyar amma a yanzu ba abinda mu ke yi''.

Abin da jami'ai ke cewa

Tahir Balarabe kakakin Hukumar Kwastam ta Najeriya reshen jihar Katsina ya ce '' da dama idan mutane sun dauki kaya cewar za su kai Jibiya daga baya sai mu gano Nijar suka kai kayan.

A cewarsa burinsu shi ne a basu dama su dinga kai manyan motoci dauke da kayan abinci Nijar.

"Akalla kananan motoci 30 su na shiga Jibiya ta hanyar Katsina da Batsari wannan ce ta sa mu ka takaita shiga da kaya Jibiya a hukumance''.

Wannan ba shi ne karon farko ba da aka samu rashin fahimta tsakanin al'ummar Jibiya musamman 'yan kasuwa da Jami'an Kwastam.

A kwanakin baya shugaban Hukumar Kwastam ya aike da tawaga ta musamman don tattaunawa da wasu daga cikin yan kasuwar yankin domin samar da matsaya kan adadin motocin da za su dinga kaiwa al'ummar kayan abinci sai dai har yanzu ba a daidaita ba.