You are here: HomeAfricaBBC2023 07 25Article 1811954

BBC Hausa of Tuesday, 25 July 2023

Source: BBC

''Ba zan sa girman kai ba don na zama kyaftin ɗin Man United''

Bruno Fernandes Bruno Fernandes

Bruno Fernandes ya ce ba zai canja ba daga ɗabi'unsa, bayan da Manchester United ta naɗa shi a mukamin kyaftin ɗin kungiyar.

Fernandes ya ja ragamar 'yan wasan United a mukamin kyaftin ɗin ta a karon farko a wasan sada zumunta da Arsenal ranar Asabar, bayan da ya maye gurbin Harry Maguire.

Tsohon kyaftin ɗin United, Garry Neville ya kira Fernandes ''abin takaici'' kan halayyar da ɗan kwallon tawagar Portugal ya nuna a karawar da Liverpool ta casa United 7-0 cikin watan Maris.

Fernandes ya ce ''Kociyan ya amince da ɗa'ar da nake da ita da kwazon da nake nunawa da kuma gogewa ta.''

Ya kara da cewar ''Ten Hag bai sanar min ba, kuma ba mu tattauna da shi cewar zai ba ni mukamin kyaftin ɗin United, domin maye gurbin Maguire ba.''

Tun bayan da Sir Alex Ferguson ya yi ritaya a 2013, United ba ta taɓa kalubalantar lashe Premier League ko Champions League ba, balle ta ɗauki kofi.

''Ya kamata Manchester United ta kara sa kwazo a dukkan kofunan da ke gabanta,'' kamar yadda Fernandes ya sanar. ''Kungiyar nan ta cancanci a yi mata hakan.''

Fernandes ya kuma amince cewar kungiyar na buƙatar karo sayo mai cin kwallaye, bayan da Anthony Martial ke yawan jinya.

Ɗan kwallon tawagar Faransa bai yi wa United wasan sada zumunta da ta ci Arsenal 2-0 ba ranar Asabar a Amurka.