You are here: HomeAfricaBBC2023 12 08Article 1895240

BBC Hausa of Friday, 8 December 2023

Source: BBC

Ba zan daina murna ba idan mun ci kwallo duk da an dakatar da ni - Arteta

Kocin Arsenal Mikel Arteta Kocin Arsenal Mikel Arteta

Mikel Arteta ya ce zai ci gaba da nuna farin cikinsa ko damuwa a kusa da layin shiga filin wasa duk da dakatarwar da aka yi masa ta wasa daya.

Kocin na Gunners ba zai jagoranci ƙungiyar ba a wasan da za ta buga ranar Asabar da Aston Villa, bayan an ba shi katin gargaɗi na uku a wannan kakar a wasan da aka tashi 4-3 tsakaninsu da Luton a ranar Talata.

Alƙalin wasa Samuel Barrot ya yanke hukuncin cewa Arteta ya yi murnar da ta wuce iyaka inda har ya shiga filin wasa bayan ƙwallon da Declan Rice ya ci.

"Ban san yadda zan iya daina hakan ba," in ji Arteta mai shekara 41.

A ranar Juma'a ya ce "Lokaci ne na farin ciki kuma kowa ya yi ta murna a filin, kuma ba ma ka sanin me kake yi ko a wane ɓangare kake na filin wasa.

"Ba daɗi hukuncin cewa yanzu ba zan kasance tare da 'yan wasana ba, amma hukunci ne da ake yankewa bisa dokar babu sani babu sabo."

Nasarar dai ta ƙara tabbatar da Arsenal a matsayinta na mai jan ragamar Premier.

Arteta ya ce ba ya son ya daina murna a bakin layin shiga fili a lokacin da suka yi nasara.

"Ina son kasancewa tare da 'yan wasana domin kullum tare muke aiki da su domin cimma abin da muke nema, wanda shi ne samun nasara kuma ku yi murna tare, a irin wannan lokaci ba ka sanin farin cikin da kake yi," in ji Arteta.

"Na san cewa akwai iyakokin da ba za ka tsallake ba, kuma dole ka girmama waɗannan iyakoki, amma idan aka ba ni dama zan tsallaka har cikinsu."

Arteta zai iya sake fuskantar hukunci bayan tuhumar da FA ta yi masa kan kalaman da ya yi bayan rashin nasarar da yi a hannun Newcastle da ci 1-0 a watan Nuwamba.

Kocin, ɗan Spain ya ce hukuncin da mai taimakawa alƙalin wasa ya yanke na karbar kwallon Newcastle "cin fuska ne" da "zubar da ƙima".