You are here: HomeAfricaBBC2024 01 01Article 1906436

BBC Hausa of Monday, 1 January 2024

Source: BBC

'Ba ɗan gudun hijirar da ke kwana a titi a Tsafe'

Zamfara na arewan Njeriya Zamfara na arewan Njeriya

Shugaban Karamar Hukumar Mulkin Tsafe da ke jihar Zamfara a Najeriya Dakta Aliyu Adamu Tsafe ya ce adadin wadanda hare-haren 'yan bindiga na baya-bayan nan suka raba da garuruwansu a yankinsa ya kai kusan dubu daya.

Sai dai ya ce tuni majalisar karamar hukumar ta dauki nauyin tsugunar da su tare da ba su tallafin abinci da kudi da kuma magunguna kuma ba wanda ya ke kwana a titi ko a tashar mota.

A hira da BBC shugaban ya musanta wasu rahotanni da ke cewa wasu daga cikin 'yan gudun hijirar sun rasa matsuguni suna watan-gaririya a gari har ma wasu na kwana a tashar mota a Tsafe.

Shugaban ya ce, ''ni mutum ne wanda a garin Tsafe nake kwana kuma nakan yi yawo da kafa ko da da daddare ne. Nakan taka kasa bayan na tashi daga ofis don in kalli al'ummana mu dan tattauna da su to tsakani da Allah abin da na sani har maganar nan babu wani dan gudun hijira mai kwana a titi kamar yadda wannan rahoto ya ce.''

Dakta Aliyu ya kara bayani da cewa, ''wani gida ne na wani bawan-Allah nan aka samam masu kashi 70 zuwa 80 na mutanen nan suke kwana.''

''Sannan akwai 'yan uwansu daman da suka dawo nan cikin garuruwan Tsafe wanda kashi 20 zuwa 25 zuwa 30 nasu su kuma suna zaune ne gidajen 'yan uwansu,'' in ji shi.

A ranar Lahadi 24 ga watan Disamba ne wasu 'yan bindiga suka kai hari kan wasu garuruwa na yankin karamar hukumar Tsafe har suka kashe mutum biyu tare da sata da barnata dukiya.

Lamarin ya sa al'ummomin garuruwa wadanda suka hada da Sungawa da Yalwa da Rakyabu gudun hijira zuwa Tsafe da sauran wurare.

Dangane da yadda har yanzu 'yan bindiga ke kisa da muzuguna wa jama'a a jihar ta Zamfara musamman yankin na Tsafe shugaban ya ce, kamar yadda aka sani daman ita wannan matsala ce da suka yi gado daga gwamnatoci na baya.

To amma ya ce suna nan suna daukar mataki na maganin matsalar tun daga tushe.

Ya ce suna nan ana bai wa jami'ai na farin kaya wadanda za su hada hannu da karfe da jami'ai na tsaro a shiga a yaki barayin don a gama da matsalar.