You are here: HomeAfricaBBC2023 02 19Article 1717361

BBC Hausa of Sunday, 19 February 2023

Source: BBC

Azpilicueta ya farfado a gadon asibiti bayan rauni ranar Asabar

Azpilicueta ya ji rauni a karawa da Southampton ranar Asabar Azpilicueta ya ji rauni a karawa da Southampton ranar Asabar

Graham Potter ya ce Kyafti, Cesar Azpilicueta ya farfado, bayan da aka kaishi asibiti, sakamakon rauni a karawa da Southampton ranar Asabar.

Azpilicueta ya fadi kasa baya motsi, bayan Sekou Mara ya doke shi da kafa a ka a gasar Premier a Stamford Bridge.

An hangi Mara na karkarwa yana tsammani raunin mai muni ne tare da wasu 'yan wasa, yayin da masu agajin gaggawa suka kai dauki da wuri.

An saka wa Azpilicueta na'urar taimakawa a yi nimfashi, kafin daga baya a fitar da shi daga fili, wanda ya suma.

Chelsea wadda ta yi rashin nasara da ci 1-0 a Borussia Dortmund a Champions League ta kara shan kashi a hannun Southampton a Premier League.

Southampton ce ta ci Chelsea 1-0 a Stamford Bridge, kuma James Ward-Prowse ne ya zura kwallo a raga.