You are here: HomeAfricaBBC2023 01 30Article 1704773

BBC Hausa of Monday, 30 January 2023

Source: BBC

Ayyukan da Shugaba Buhari ya ƙaddamar a Kano

Shugaba Muhammadu Buahri Shugaba Muhammadu Buahri

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da jerin ayyuka a birnin Kano.

Shugaban ya samu rakiyar wasu daga cikin ƴan majalisar ministocinsa zuwa birnin na Kano.

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ne ya karɓi shugaban tare da Ministan Sufuri Mu'azu Jaji Sambo.

Ƙaddamar da ayyukan na zuwa ne ƙasa da mako guda bayan da shugaban ya ƙaddamar da wasu ayyukan a jihar Katsina.

Wasu daga cikin ayyukan, gwamnatin jihar Kano ce ta yi su, yayin da wasu kuma na gwamnatin tarayya ne.

Ayyuka takwas ne shugaban ya ƙaddamar a jihar Kano, cikin tsauraran matakan tsaro.

Cikin ayyukan akwai Gadar nan mai hawa-hawa ta Hotoro da Cibiyar kula da masu larurar ciwon daji da cibiyar adana bayanai ta 'Galaxy Backbone' da tashar sauke kaya ta kan tudu wato 'Dala Inland Dry Port'.

Haka kuma akwai tashar samar da lantarki ta hasken rana da ke Chalawa sai kuma cibiyar horas da sana'o'i ta Aliko Dangote da ke kan titin Zariya da kuma rukunin gidaje da ke Gandun Sarki a Darmanawa.

Haka kuma shugaban ya ƙaddamar da wani sabon sashe daga cikin fadar sarkin Kano.

Yayin ƙaddamar da waɗannan ayyuka, wasu daga cikin jama'ar birnin sun fito sun yi wa shugaban dafifi, wasu kuma sun yi zamansu a gida kasancewar an rurrufe wasu hanyoyin cikin garin musamman wuraren da shugaban zai bi.

Sannan an jibge jami’an tsaro a kowacce kusurwa da manyan titunan birnin.

Wasu wuraren da Shugaba Buharin ya je a Kanon ya je su ne a cikin jirgi mai saukar ungulu.

Sannan kuma an samu wasu rahotanni da suka tabbatar an samu hatsaniya da kuma bore a wasu sassa na jihar bayan ƙaddamar da ayyukan da shugaban ya yi.