You are here: HomeAfricaBBC2023 07 20Article 1808786

BBC Hausa of Thursday, 20 July 2023

Source: BBC

Australia ta yi nasara kan Ireland

Yan wasan Australia a murna Yan wasan Australia a murna

Fenaretin da Steph Catley ta ci bayan hutun rabin lokaci ya bai wa Australia mai masaukin baki nasara kan Jamhuriyar Ireland da ci 1-0 a gasar cin kofin duniya.

Catley, wadda ke a matsayin kyaftin bayan taurariyar 'yar wasan Australia Sam Kerr ta samu rauni, ta jefa kwallon a raga a minti na 52 da fara wasa.

Kerr, wadda ita ba za ta buga wasan Australia na biyu da Najeriya ba, ta zauna a benci tare da abokan wasanta amma ta takaita murnar ta saboda gudun fama raunin da take jinya a halin yanzu.

'Yan wasan Irelend Megan Connolly da Katie McCabe da Louise Quinn duk sun kusa jefa kwallo a ragar Australia amma masu masaukin bakin sun dage wurin tare gida inda suka tabbatar da cewa sun fara gasar cin kofin duniyar da nasara.

Yanzu Australia za ta kara da Najeriya a ranar 27 ga watan yuli a wasanta na gaba.