You are here: HomeAfricaBBC2021 03 12Article 1202560

BBC Hausa of Friday, 12 March 2021

Source: BBC

Arsenal za ta rama abin da Olympiakos ta yi mata a bara a Europa

Arsenal ta je ta doke Olympiakos da ci 3-1 a wasan zagayen farko Arsenal ta je ta doke Olympiakos da ci 3-1 a wasan zagayen farko

Arsenal ta je ta doke Olympiakos da ci 3-1 a wasan zagayen farko a gasar Europa League da suka kara a kungiyoyi 16 da suka rage a gasar.

Martin Odegaard ne ya fara ci wa Gunners kwallo daga yadi na 20, sai Youssef El-Arabi ya farke wa Olympiakos kwallo, wasa ya koma 1-1.

Daga nan ne Arsenal ta kara sa kaimi ta zura kwallo biyu ta hannun Gabriel Magalhaes da kuma Mohamed Elneny.

A kakar bara Olympiakos ce ta fitar da Arsenal daga gasar Turai, bayan da Gunners ta ci 1-0 a Girka ranar 20 ga watan Fabrairun 2020.

Sai dai a wasa na biyu ranar 27 ga watan Fabrairun 2020, Olympiakos ta je Emirates ta ci 2-1 da hakan ya sa aka fitar da kungiyar a gasar bara.

Gunners za ta karbi bakuncin wasa na biyu ranar 18 ga watan Maris a Emirates.

Arsenal wadda take ta 10 a teburin Premier League na fatan lashe kofin Europa na bana, domin ta samu gurbin buga gasar badi kai tsaye.