You are here: HomeAfricaBBC2023 09 04Article 1837793

BBC Hausa of Monday, 4 September 2023

Source: BBC

Arsenal za ta karɓi bakuncin Man United a Emirates

Arsenal da Man united Arsenal da Man united

Manchester United za ta ziyarci Arsenal a Emirates, domin buga wasan mako na huɗu a gasar Premier League ranar Lahadi.

Arsenal ta ci Nottingham Forest 2-1 da yin nasara a kan Crystal Palace 1-0 da kuma tashi 2-2 da Fulham a gasar Premier League.

Ita kuwa Manchester United ta ci Wolves 1-0 da rashin nasara 2-0 a gidan Tottenham da doke Nottingham Forest 3-1 a babbar gasar tamaula ta Ingila a bana.

Abin da ya kamata ku sani

Arsenal ta ci wasa huɗu da canjaras ɗaya a wasa biyar da ta karɓi baƙuncin United har da karawa biyu baya.

Watakila Gunners ta ci United wasa uku a jere a karon farko tun bayan 1988 da kuma 1991.

Manchester United ta yi rashin nasara a karawa tara da ta hadu da Arsenal da canjaras biyu da cin wasa biyu.

Kungiyar da ke gida kan ci kwallo akalla uku a wasa biyu da suka fafata a tsakaninsu.

Arsenal

Arsenal ta yi rashin nasara biyu daga wasa 24 Premier League da ta yi a gida da cin karawa 18 da canjaras hudu.

Wasa hudu ne daga 26 da Arsenal ta buga a gida ba tare da kwallo ya shiga ragarta ba.

Cikin wasa 22 da Arsenal ta fuskanci kungiyar da ke amsa United a Premier League a gida ta ci karawa 19 da canjaras uku, wato a haɗuwa da Leeds da Manchester da Newcastle da Sheffield da kuma West Ham ba tare da rashin nasarar ba.

Kwallo 12 daga 16 da aka ci Arsenal a Emirates, an zura musu ne a zagaye na biyu, yayin da hudu daga ciki a farko-farkon wasa aka zura musu a raga.

Watakila Bukayo Saka ya zama dan wasan Arsenal na farko da zai ci United kwallo a wasa huɗu a jere a Premier League.

Manchester United

Manchester United ta ci wasa shida daga bakwai baya da ta buga a Premier League.

Watakila United ta yi rashin nasara a wasa biyu a waje a jere da fara Premier a karon farko tun bayan 1973-74, kakar da ta fadi daga babbar gasar tamaula ta Ingila.

Wasa daya United ta yi nasara daga 10 da ta ziyarci Landon da canjaras uku da rashin nasara shida, shine wanda ta ci Fulham 2-1 a watan Nuwamba.

Bruno Fernandes ya ci kwallo uku a wasa biyar baya a Premier League a Manchester United, bayan cin daya daga fafatawa 15.

Marcus Rashford yana da hannu a cin kwallo hudu daga biyar da United ta ci Arsenal a kakar bara.