You are here: HomeAfricaBBC2023 03 09Article 1728014

BBC Hausa of Thursday, 9 March 2023

Source: BBC

Arsenal ta tashi 2-2 a gidan Sporting a Europa League

Yan wasan Arsenal Yan wasan Arsenal

Sporting Lisbon da Arsenal sun tashi 2-2 a wasan farko zagayen 'yan 16 a Europa League da suka fafata a Portugal.

Minti 22 da fara wasa Arsenal ta zura kwallo a raga ta hannun William Saliba, sai dai minti 12 tsakani Sporting ta farke ta hannun Goncalo Inacio.

Bayan da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu ne Sporting ta kara na biyu ta hannun Paulinho a minti na 10.

Arsenal ta farke na biyu ta hannun Hidemasa Morita, wanda ya ci gida.

Dukkan kungiyoyin sun sami damar cin kwallaye, amma hakan wasan ya tashi 2-2.

Wannan shine karo na biyar da suka yi tata burza a tsakaninsu, Arsenal ta ci biyu da canjaras uku.

Ranar Alhamis 16 ga watan Maris, Gunners za ta karbi bakuncin wasa na biyu a Emirates, inda za a tantance wadda za ta kai quater finals.

Ranar Lahadi 12 ga watan Maris, Arsenal za ta ziyarci Fulham domin buga wasan Premier League.

Gunners tana matakin farko a kan teburin bana a babbar gasar Premier League.