You are here: HomeAfricaBBC2023 08 02Article 1817399

BBC Hausa of Wednesday, 2 August 2023

Source: BBC

Arsenal ta shirya da Raya, City na son maye gurbin Mahrez da Doku ko Olise

David Raya David Raya

Arsenal ta amince da rattaba hannu kan mai tsaron ragar Brentford David Raya, mai shekara 27, inda kungiyar ta Sifaniya ta sanya farashin fam miliyan 40. (Evening Standard)

Manchester City na son dauko dan wasan Belgium Jeremy Doku, mai shekara 21 da zai maye gurbin Riyad Mahrez, wanda ya koma kungiyar Al-Ahli ta kasar Saudiyya da taka leda a makon da ya wuce. (Fabrizio Romano)

Manchester City dai ta zuba ido kan dan wasan gaba na Crystal Palace Michael Olise, mai shekara 21, da shi ma ta ke ganin zai iya maye gurbin Mahrez idan ciniki bai fada da Doku ba. (Fabrizio Romano)

Mai kungiyar Cystal Place Roy Hodgson ya amince abu ne mai wuya dan wasan Faransar ajin shekara 21 ya ci gaba da taka leda a kulub din a kakar da mu ke ciki. (Athletic - subscription required)

An yi watsi da tayin fam miliyan 85 da Bayern Munich ta sanya kan dan wasan Tottenham kuma mai kai hari na Ingila, Harry Kane has been turned down, inda Spurs ta bukaci fam miliyan 100 kan dan wasan mai shekara 30. (Independent)

West Ham ta hakura da batun daukar dan wasan Southampton, kuma na tsakiyar Ingila James Ward-Prowse, sakamakon makudan kudin da kungiyarsa ta sanya idan har za ta saida dan wasan mai shekara 28. (Sky Sports)

Dan wasan Portugal mai taka leda a Manchester City, Carlos Borges, mai shekara 19, na gab da komawa Ajax kan farashin fam miliyan 20. (£17m). (Athletic - subscription required)

Everton ka iya shiga tawagar zawaran dan wasan West Ham, kuma mai kai hari na Jamaica Michail Antonio, bayan dan wasan mai shekara 33 ya yi rashin nasarar komawa Saudiyya da taka leda.(Football Insider)

Galatasaray na nuna sha'awar dan wasan tsakiya na Fransa, mai taka leda a Tottenham Tanguy Ndombele, mai shekara 26 kan farashin fam miliyan 11. (Mirror)

Watakil Leeds ta farauto dan wasan Manchester United da Ingila Brandon Williams mai shekara 22. (Independent)