You are here: HomeAfricaBBC2023 12 17Article 1900169

BBC Hausa of Sunday, 17 December 2023

Source: BBC

Arsenal ta koma ta daya a teburin Premier kafin wasan Liverpool

Kai Harvetz Kai Harvetz

Arsenal ta yi nasarar doke Brighton ta kuma hau kan teburin Premier, kafin Liverpool ta buga wasa da Manchester United ranar Lahadi.

Gunners ta koma ta daya a kan teburin babbar gasar tamaula ta Ingila, bayan da ta yi nasarar cin 2-0 ta hannun Gabriel Jesus da kuma Kai Havertz.

Arsenal ce ta mamaye zagayen farko, amma ba ta samu zura kwallo ba har sai dai ta kai Jesus ya zura na farko a raga.

Brighton ta kusan zare kwallon da aka zura mata, lokacin da Pascal Gross ya buga kwallo amma ya yi fadi, daga nan Havertz ya kara na biyu a raga.

Brighton, wadda ta yi fatan doke Arsenal karo na uku a jere a Emirates, ba ta taka rawar gani ba sosai, wadda kwallo daya ta buga ya nufi raga.

Da wannan sakamakon Gunners ta koma ta daya a teburin Premier League da maki 39.

Aston Villa ta koma ta biyu da maki 38, bayan da ta je ta yi nasara a kan Brentford da cin 2-1a ranar ta Lahadi.

Idan Liverpool ta ci Manchester United za ta karbe matakin farko, amma idan ta yi canjaras za ta zama ta biyu, idan aka doke ta kuwa za ta zama ta uku.