You are here: HomeAfricaBBC2023 09 17Article 1845860

BBC Hausa of Sunday, 17 September 2023

Source: BBC

Arsenal ta kawo karshen kasa cin wasa a gidan Everton

Hoto daga gasar Hoto daga gasar

Everton ta yi rashin nasara da ci 1-0 a hannun Arsenal a wasan mako na biyar a Premier League ranar Lahadi a Goodison Park.

Kungiyoyin biyu sun kammala zagayen farko ba ci, yayin da suka koma zagaye na biyu ne Leandro Trossard ya ci wa Gunners kwallo.

Gunners, wadda ta maye gurbin golan tawagar Ingila, Aaron Ramsdale a wasan da David Raya - ta yi rashin nasara a wasa huɗu baya daga biyar da ta ziyarci Everton.

Arsenal ta yi wasa 12 a waje kenan ba tare da an zura mata kwallo a raga ba a Premier League tun daga fara kakar bara.

Fulham da Manchester City sune ke biye da Gunners a irin wannan bajintar da kowacce ke da bakwai-bakwai.

Da wannan sakamakon Arsenal ta haɗa maki 13 tana mataki na huɗu, iri ɗaya da wanda Tottenham ta biyu da kuma Liverpool ta uku.

Ranar 24 ga watan Satumba Arsenal za ta karɓi bakuncin Tottenham a karawar mako na shida a Premier League.

Kafin nan Gunners za ta buga Champions League ranar 20 ga watan Satumba, inda PSV Eindhoven za ta ziyarci Emirates.

Wasa hudu da suka kara a kaka biyu baya:

2022/2023

Premier League Laraba 1 ga watan Maris 2023

  • Arsenal 4 - 0 Everton


  • Premier League Asabar 4 ga watan Fabrairun

  • Everton 1 - 0 Arsenal


  • 2021/2022

    Premier League Lahadi 22 ga watan Mayun 2022

  • Arsenal 5 - 1 Everton


  • Premier League Litinin 6 ga watan Disamba 2021

  • Everton 2 - 1 Arsenal