You are here: HomeAfricaBBC2021 03 19Article 1209052

BBC Hausa of Friday, 19 March 2021

Source: BBC

Arsenal ta kai quarter finals a Europa karo hudu a kaka biyar

Gunners din ta kai matakin quarter finals a gasar ta zakarun Turai Gunners din ta kai matakin quarter finals a gasar ta zakarun Turai

Arsenal ta kai wasan daf da na kusa da na karshe a Europa League na bana, duk da rashin nasara da ci 1-0 a hannun Olympiakos a Emirates.

Gunners din ta kai matakin quarter finals a gasar ta zakarun Turai, bayan da ta ci 3-1 a wasan farko, jumulla ta ci kwallo 3-2 gida da waje kenan.

Kungiyoyin biyu sun kammala minti 45 din farko ba ci ranar Alhamis, bayan da sukla yi hutu suka koma karawar zagaye na biyu Youssef El-Arabi ya ci wa Olympiakos kwallon.

Arsenal ta barar da damarmakin cin kwallaye a wasan da ta sa kyaftin dinta Pierre-Emerick Aubameyang, wanda ta ajiye a karawa da ta doke Tottenham 2-1 a gasar Premier League ranar Lahadi.

Sai dai Olympiakos ta karkare karawar da yan kwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Ousseynou Ba jan kati saura minti bakwai a tashi daga wasan.

Ranar Juma'a za a raba jadawalin wasannin quarter finals da na daf da karshe a gasar ta zakarun Turai ta Europa ta kakar bana.

Arsenal tana ta 10 a teburin Premier League da maki 41, bayan buga wasa 28 a gasar.

Gunners na bukatar lashe Europa Cup na bana, idan har tana son zuwa gasar badi cikin ruwan sanyi.