You are here: HomeAfricaBBC2023 10 25Article 1869023

BBC Hausa of Wednesday, 25 October 2023

Source: BBC

Arsenal na son Douglas Luiz, Álvarez zai ci gaba da zama a Man City

Dan wasan tsakiyar Brazil Douglas Luiz Dan wasan tsakiyar Brazil Douglas Luiz

Har yanzu Arsenal na son dan wasan tsakiyar Brazil Douglas Luiz mai shekara 25 daga Aston Villa, do da yake a baya ta sha taya ɗan wasan ana watsi da tayin nata. (90min)

Everton na nuna damuwa kan rahotannin da ke cewa Al-Ettifaq ta Saudiyya na son ɗan wasanta ɗan Ingila Dominic Calvert-Lewin mai shekara 26, yayin da har yanzu ƙungiyar ba ta san inda ta dosa ba a kakar bana.(Football Insider)

Manchester United ta bar ƙofarrta a buɗe kan duk wani ta yi da ta samu game da Jadon Sancho mai shekara 23, wanda alamu ke nuna zamansa ya ƙare a ƙungiyar.(Fabrizio Romano, via Sun)

Ɗan wasan Fiorentina da Argentina Nicolas Gonzalez mai shekara 25, na ci gaba da ɗaukar idanun ƙungiyoyin Premier bayan ƙoƙarin da ɗan wasan ya fara a kakar bana. (La Gazzetta dello Sport - in Italian)

West Ham na bibiyar ɗan wasan Girka da AZ Alkamaar Vangelis Pavlidis mai shekara 24 saboda suna son ƙara wa gabanta ƙarfi.(90min)

Manchester City na a shirye take da duk wani tayi da za a yi mata kan ɗan wasanta na tsakiya ɗan Ingila Kalvin Phillips mai shekara 27, wanda ake sa ran zai iya barin ƙungiyar a watan Janairu saboda ya gaza samun gurbi ƙarƙashin Pep Guardiola. (Fabrizio Romano)

Sevilla na zuba ido domin ganin inda ɗan wasan Manchester United ɗan Tunisia Hannibal Mejbri mai shekara 20 zai dosa.(Caught Offside)

Manchester City na da kwarin gwiwa cewa ɗn wasanta ɗan Argentina Julian Alvaresz mai shekara 23 zai ci gaba da zama a ƙungiyar, duk kuwa da rahotannin da ke cewa Barcelona da Real Madrid na nuna sha'awarsu kan ɗan wasan. (Football Insider)

Kocin Bournemouth Andoni Iraola na fuskantar ƙananan maganganu a wannan makon, kuma zai iya zama koci na farko da za a kora a Premier a wannan kakar.(Sun)

Newsleading news icon

Sportsleading sports icon

Businessleading business icon

Entertainmentleading entertainment icon

Africaleading africa news icon

Opinionsleading opinion icon