You are here: HomeAfricaBBC2023 09 30Article 1854017

BBC Hausa of Saturday, 30 September 2023

Source: BBC

Arsenal na sa ido kan Dembele, PSG na son karkatar da hankalin Madrid daga kan Mbappe

Ousmane Dembele Ousmane Dembele

Arsenal da Tottenham da kuma West Ham na sa ido kan dan wasan gaba na Paris St-Germain da Faransa Ousmane Dembele don dakko shi a matsayin aro. Dan wasan mai shekaru 26 ya koma zakarun Faransa ne a bazara daga Barcelona. (Sunday Mirror)

Dan wasan gaban Ingila Ivan Toney ya shirya barin Brentford a watan Janairu. Kulob din na son barin dan wasan mai shekaru 27, wanda ke zaman dakatarwa na tsawon watanni takwas saboda saba ka'idojin Hukumar shirya gasar ca-car Kwallon Kafa ta Ingila, idan har aka biya ta fam miliyan 60. (Sunday Mirror)

Dan wasan tsakiya na Newcastle da Brazil Bruno Guimaraes ya amince da tsawaita kwantiraginsa. Mai shekaru 25 a duniya, zai tsawaita kwantiragin na sa ne zuwa 2028. (Sky Sports)

Manchester United ta yi kokarin musayar 'yan wasa da dama da suka hada da dan wasan tsakiya dan kasar Holland Donny van de Beek mai shekaru 26 da kuma dan wasan tsakiya na Brazil Fred mai shekaru 30, a matsayin hanyar daidaita farashin sayen Rasmus Hojlund. Amma Atalanta tana sha'awar ganin an ba ta tsabar kuɗi ne kawai. A kan dan wasanta mai shekaru 20. (The Athletic)

Van de Beek ya ja hankalin Villarreal bayan ya kasa samun tagomashi a Manchester United. (Fichajes)

United ta kuma fara tattaunawa da dan wasan Tunisia Hannibal Mejbri, mai shekara 20, kan sabon kwantaragi. (Sunday Express)

Everton za ta yi kokarin sake tattaunawa kan batun cinikin Dele Alli mai shekara 27 daga Tottenham inda Spurs za ta karbi fam miliyan 10 idan ya zarce wasanni 20 a Everton. (Sunday Express)

Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar West Brom ta kara zage damtse wajen neman sabon mamallaki, inda mai kungiyar na yanzu Guochuan Lai wanda dan China ne ke neman siyar da ita kafin karshen shekarar nan. (Mail Sunday)

Chelsea da Bayern Munich na ci gaba da sha'awar siyan golan Ingila da Arsenal Aaron Ramsdale, mai shekara 25, wanda ya rasa matsayinsa na babban golan kungiyar. (Mail Sunday)

Shugaban Tottenham Daniel Levy ya ce kofa a bude take don siyar da kashi 25% na hannun jarin kungiyar. (Sunday Times)

Sai dai bayanai na cewa duk da rasa gurbin na sa, Ramsdale ba ya tunanin hanzarta barin Arsenal, kana bai fara tunanin yanke shawara kan makomarsa ba tukuna. (Sunday Mirror)

Manchester United, da Liverpool da Arsenal sun shirya tsaf, don don fara neman dan wasan Brentford da Scotland Aaron Hickey, mai shekara 21. (Sunday Mirror)

Dan wasan gaba na Brighton da Jamhuriyar Ireland Evan Ferguson ya yanke shawarar ci gaba da zama tare da Seagulls, maimakon komawa Manchester United da ta nuna sha’awar daukarsa a lokacin bazara. (Sunday Mirror)

Paris St-Germain na zawarcin dan wasan gaban Real Madrid da Brazil Rodrygo, mai shekara 22, da zummar karkatar da hankalin Madrid din da ke neman dan wasan gabanta Kylian Mbappe, mai shekara 24. (Football Transfers)

Har ila yau Madrid tana sha'awar sayen dan wasan baya na kasar Canada Alphonso Davies, mai shekara 22, daga Bayern Munich. (Football Transfers)