You are here: HomeAfricaBBC2023 09 26Article 1851641

BBC Hausa of Tuesday, 26 September 2023

Source: BBC

Arsenal na matsa ƙaimi kan Toney, Roma na son riƙe Lukaku, ana shirin sasanta Sancho da Ten Hag

Ivan Toney Ivan Toney

Arsenal ta shirya tsaf domin kara kaimi wajen zawarcin dan wasan gaban Ingila Ivan Toney a watan Janairu, Brentford ta sa ma dan wasan mai shekaru 27 farashin fan miliyan 60. (Mirror)

Brentford na tunanin siyan sabon dan wasan gaba a watan Janairu ko da ba za su sayar da Toney ba, inda bayanai ke cewa kungiyar na sa ido a kan dan was an Wolfsburg dan kasar Denmark Jonas Wind, mai shekara 24, da AZ Alkmaar na Girka mai shekara 24, Vangelis Pavlidis da dan wasan Santos na Brazil Marcos Leonardo, mai shekara 20 a jerin sunayensu. (90Mints)

Roma na kokarin ganin ta rike Romelu Lukaku mai shekaru 30 da ta dakko aro daga Chelsea don zama dan wasanta na din-din-din. Wasu rahotanni na cewa a shirye take ta bayar da dan wasanTA dan Ingila Ingila Tammy Abraham, mai shekara 25 a matsayin musaya. (Calciomercatoweb)

Shugaban Inter Milan Beppe Marotta ya ce nan ba da jimawa ba kungiyar za ta gana da dan wasan bayan Italiya Federico Dimarco, mai shekara 25, domin tattaunawa kan sabon kwantaragi. (Radio Anch'Io Sport)

Dan wasan bayan Ingila Fikayo Tomori, mai shekara 25, ya ki amincewa da ci gaba da zama a AC Milan har lokacin bazara. (Calciomercato)

Abokan wasan Jadon Sancho na Manchester United sun bukaci dan wasan Ingila, mai shekara 23, da ya nemi afuwa tare da kawo karshen takaddamar da ke tsakaninsa da kocin kungiyar Erik ten Hag. (Mirror)

Kungiyar kwararrun ‘yan wasan kwallon kafa (PFA) ta yi tayin taimakawa a wani yunkuri na taimakawa Ten Hag da Sancho su sasanta tsakaninsu. (Times)

West Ham ta kawo karshen sha'awarta ta daukar dan wasan Ingila Jesse Lingard a matsayin kyauta, mai shekaru 30 a yanzu yana horar da kulob din Al Ettifaq na gasar ajin matsakaita ta Saudiyya. (The Athletic)

Ana zargin hukumar Uefa da gabatar da shaidun “cikakkiyar rashin gaskiya” ga wani bincike mai zaman kansa kan hargitsin da ya faru a wasan karshe na gasar cin kofin zakarun Turai na 2022 tsakanin Liverpool da Real Madrid a birnin Paris. (The Athlentic)