BBC Hausa of Wednesday, 12 October 2022

Source: BBC

Arnold da Matip na Liverpool za su yi jinyar kusan mako uku

Alexander-Arnold da Matip sun ji rauni a wasan Premier League karawa da Arsenal Alexander-Arnold da Matip sun ji rauni a wasan Premier League karawa da Arsenal

Ana sa ran mai tsaron bayan Liverpool, Trent Alexander-Arnold da Joel Matip za su yi jinyar mako biyu zuwa uku. Alexander-Arnold da Matip sun ji rauni a wasan Premier League karawa da Arsenal ta hada maki uku a kan kungiyar Anfield. Shi kansa Luis Diaz ya ji rauni a wasa da Gunners, wanda ake sa ran sai cikin watan Disamba zai koma fagen fama. Liverpool ta yi rashin nasara da ci 3-2 a hannun Arsenal a Emirates a babbar gasar tamaula ta Ingila ranar Lahadi. Hakan ne ya sa Liverpool ke mataki na 10 a teburi da maki 10 da tazarar maki 14 tsakaninta da Gunners, wadda take ta daya a kan teburin gasar bana. Kungiyar da Jurgen Klopp ke jan ragama za ta yi karawa shida nan da karshen watan Oktoba. har da wanda za ta karbi bakuncin Manchester City. 'Yan wasan Liverpool da ke jinya sun hada da Arthur Melo da Alex Oxlade-Chamberlain da Naby Keita da kuma Andrew Robertson. Curtis Jones ya koma atisaye, wanda ake sa ran watakila ya buga wasan da Liverpool za ta yi da Rangers a Champions League ranar Laraba.