You are here: HomeAfricaBBC2023 09 04Article 1837709

BBC Hausa of Monday, 4 September 2023

Source: BBC

Apple ya bi umarnin sake nau'in caza a sabbin wayoyinsa

Hoton alama Hoton alama

Sabon samfurin wayar iPhone mallakin Apple zai ƙunshi caza iri ɗaya da ta Samsung lokacin da za a fitar da shi a ranar 12 ga watan Satumba.

A halin yanzu, wayoyin kamfanin suna amfani da caza ta daban, saɓanin na takwarorinsu, ciki har da Samsung.

Dokar Tarayyar Turai ta buƙaci kamfanoni masu ƙera waya da su rungumi hanyar amfani da caza iri ɗaya ta gama-gari nan da watan Disamban 2024 don rage yawan kuɗin da mutane ke kashewa.

Yawancin sabbin wayoyin Apple kamar na iPads sun riga sun fara amfani da irin cazar, amma kamfanin ya yi jayayya da dokar ta EU.

Lokacin da aka ɓullo da dokar a watan Satumban 2021, wani wakilin Apple ya shaida wa BBC cewa: "Tsarin doka da ke bayar da izinin amfani da nau'in caza iri ɗaya yana hana cigaban ƙirƙira maimakon ƙarfafa shi, wanda hakan zai cutar da masu saye a Turai da ma duniya baki ɗaya."

Tuni wasu daga cikin kamfanonin ƙera waya suka fara amfani da caza iri ɗaya kamar Amazon, kuma dukkan wayoyin iPhone tun daga iPhone 8, wadda aka ƙaddamar a 2017, na da damar yin caji ba tare da jona waya ba.

A yanzu iPhone 14 na iya zama ta karshe da za ta yi amfani da wata caza, inda hakan zai kawo karshen amfani da cazar mai walkiya - wanda ake sayarwa a kantin Apple kan fan 19.

Babu tabbacin ko wannan zai kawo sauyi ga nau'in cazar a duniya, kodayake katafaren kamfanin ba zai iya yin wani nau'i na wayar hannu ba don kasuwar Turai kaɗai.

Ana sa ran ganin sauye-sauye a sabbin wayoyin iPhone 15 da iPhone 15 Pro waɗanda za su fito kasuwa a mako mai zuwa a taron da kamfanin ke gudanarwa na shekara-shekara.

A cewar rahoton Bloomberg, fa'idodin sauya cazar ga masu amfani da shi zai ba su damar yin amfani da caza iri ɗaya a iPads, Macs da iPhone, waɗanda kuma ke da saurin intanet.