You are here: HomeAfricaBBC2023 03 30Article 1740812

BBC Hausa of Thursday, 30 March 2023

Source: BBC

Ana tuhumar mutum takwas da laifin tayar da gobarar da ta kashe 'yan ci-rani a Mexico

An ce biyar daga cikin wadanda ake zargin jami'an tsaro ne a cibiyar da ke Ciudad Juarez An ce biyar daga cikin wadanda ake zargin jami'an tsaro ne a cibiyar da ke Ciudad Juarez

Masu gabatar da kara na Mexico sun ce sun gano mutane takwas da ake zargi da mutuwar mutum 38 a wata gobara da ta tashi a cibiyar tsare yan ci-rani.

Biyar daga cikin wadanda ake zargi an ce masu gadi ne a cibiyar da ke birnin Ciudad Juarez, wanda ke kan iyakar Mexicon da Amurka.

Yanzu ana binciken wannan gobara a matsayin laifin kisan kai.

Tun bayan da wannan mummunan al'amari ya faru a wannan cibiya hukumomi ke ci gaba da fuskantar matsin lamba kan su bayyana dalilin da ya sa ba a bude 'yan ci ranin ba wadanda suka fito daga yankin Amurka ta tsakiya da kuma Latin Amurka.

Shugaban Mexicon Andrés Manuel López Obrador ya ce duk wadanda ke da hannu a lamarin za su fuskanci hukunci daidai da yadda doka ta yi tanadi.

Da yake magana a wani taron manema labarai shugaban ya bayar da tabbacin cewa za a yi bincike ba tare da wata rufa-rufa ba, kuma ba sani ba sabo.

Jim kadan bayan gobarar Mista Lopez Obrador ya ce yan ci-ranin sun cinna wa katifu wuta lokacin da suka fahimci cewa za a mayar da su kasashensu.

Akwai rahotannin da ke nuna cewa an tsare yan ci-ranin a wani yanayi maras kyau kuma ba a ba su isasshen ruwan sha lokacin da suke tsare ba.

Wani abu daya da ake ta tambaya a kasar ta Mexico musamman ma sauran ‘yan ci-ranin da ke garin da gobarar ta tashi da kuma masu rajin kare hakki, shi ne, me ya sa masu gadi suka ki bude tsararrun lokacin da gobarar ta tashi?

An ce an ga wani hoton bidiyo dan takaitacce na tsawon dakika talatin daga wata kyamara ta tsaro, wanda a hoton aka ga akalla wani mutum daya da ya yi kokarin bude kofar inda mutanen ke tsare.

Yayin da sauran masu gadin suke ta kai-komo a waje kafin su bar wutar ta kama dakin gaba daya.

Wannan hoton bidiyo ya karade shafin Twitter kuma jaridun Mexico da dama sun wallafa shi, inda mutane da dama ke nuna mamaki da takaicinsu a kan abin da suka ce gazawar jami’an tsaron wurin wajen hana salwantar rayuwar mutanen.

Da aka yi wa Shugaban kasar, wanda kusan ba ya ga maciji da kafafen yada labarai sai ya zargi 'yan jarida da neman zuzuta abu su kara masa gishiri maimakon su nuna tausayi ga wadanda gobarar ta rutsa da su a cewarsa.

Jami’an Mexico sun ce akwai jumullar mutane 68 a cibiyar a lokacin gobarar.

Yawancinsu 'yan kasar Guatemala, ne saura kuma daga Colombia da Ecuador da El Salvador da Honduras da kuma Venezuela.

Hukumomi sun ce an fitar da sunayen mutanen amma ba a fayyace wadanda suka rasu da wadanda suka ji raunuka ba.

Gobarar ta tashi ne a lokacin da Mexico ke fama da matsalar 'yan ci-rani da ke shiga yawanci domin su tsallaka zuwa Amurka.