You are here: HomeAfricaBBC2023 02 17Article 1716419

BBC Hausa of Friday, 17 February 2023

Source: BBC

Ana cigiyar wani biloniya da ya ɓace a China

Mista Bao, babban dillali ne a China Mista Bao, babban dillali ne a China

Ɗaya daga cikin hamshaƙan attajirai na ƙasar China ya yi ɓatan-dabo, kamar yadda kamfaninsa ya bayyana.

Ba a dai ji ɗuriyar Bao Fan ba a cikin 'yan kwanakin nan , wanda ya kasance shugaban kamfanin hada-hadar kuɗi na China Renaissance Holdings, in ji kamfanin a ranar Alhamis.

Mista Bao, babban dillali ne a China wanda abokan cinikinsa suka haɗa da manyan kamfanonin fasaha na Didi da Meituan.

Sanarwar da kamfaninsa ya fitar ta sake nuna damuwa game da yiwuwar da ake yi na cewa hukumomin China sun fara kama hamshakan mutane musamman a bangaren hada-hadar kuɗi.

Hannayen jari a kamfanin sun yi kasa a ranar Juma'a, bayan da ya shaida wa masu hannun jarin cewa "sun kasa tuntuba ko ji daga wajen mista Bao Fan ".

Hukumar ta ƙara da cewa ba ta da masaniyar "duk wani bayani da ke nuna cewa rashin samun Mista Bao na da alaƙa da kasuwanci ko ayyukan kungiyar".

Lokacin da aka nemi ƙarin bayani, kamfanin ya buƙaci BBC ta je zuwa kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Hong Kong.

Kamfanin bai bayyana tsawon lokacin da mista Bao ya ɓace ba.

Kamfanin dillancin labaran kasuwanci na ƙasar China, Caixin, ya ambato majiyoyin da ke cewa ma'aikatan ba su samu damar tuntuɓar sa ba tsawon kwanaki biyu.

Caixin ta kuma ruwaito cewa hukumomi sun kama shugaban kamfanin, Cong Lin a watan Satumban da ya gabata kan aikin da ya yi a baya a bankin ICBC na gwamnati.

Kamfanin Renaissance na China bai ce komai ba game da halin da mista Cong ke ciki.

Yanzu babu sunan shi a matsayin mai zartarwa a kamfanin da kuma a cikin rahotonsa na wucin-gadi na baya-bayan nan.

Ɓacewar mista Bao - ɗaya daga cikin hamshakan ‘yan kasuwa a China – ya sake dawo da batun yawan ɓacewar manyan mutane na tsawon lokaci ba tare kuma da samun wani bayani ba a China.

Akalla hamshakan biloniyoyi 12 suka ɓace na tsawon lokaci a cikin shekaru kalilan da suka wuce bayan takun saka da jam’iyya mai mulki ta kwamunisanci, a cewar mujjalar Forbes.

A wasu lamura daban-daban, manyan masu arziki sun yi ɓatan dabo akasari kan binciken cin hanci da rashawa da kuma matakan da China ke ɗauka kan kamfanonin fasaha na ƙasar.

Shahararrun mutane da a baya suka ɓata sun haɗa da wanda ya kafa ƙungiyar Fosun, Guo Guangchang, wanda ya ɓace na tsawon kwanaki 2015.

A shekarar 2017 ma, an kama Xiao Jianhua, ɗan kasuwar ƙasar China, haifaffen Canada, inda a shekarar da ta gabata aka ɗaure shi da laifin cin hanci da rashawa.

A karshen 2020, wanda ya kafa kamfanin Alibaba, Jack Ma, shi ma ya ɓace na tsawon watanni uku, bayan ya soki masu kula da kasuwanni.

An sa rai cewa zai fito bainar jama'a don ya lissafa hanyoyin biyan kuɗin kamfaninsa na intanet - wanda da alama zai iya sa ya zama mafi arziki a China.

Ana ɗaukar mista Bao a matsayin babban mutum a bangaren kasuwanci a China, bayan da ya aiwatar da wasu manyan haɗaka da suka haɗa da Didi da Kuaidi, da shafukan kai sakon abinci da aka saya Meituan da Dianping.

Ya kafa kamfanin China Renaissance a shekarar 2005, inda tun daga lokacin ya zama babbar cibiyar hada-hadar kuɗi a ƙasar.

Bankin ya yi aiki a matsayin mai bayar da shawara don fara bayar da kyauta ga jama'a na shafukan kasuwanci na intanet JD.com da Kuashou, da kuma saka suna Didi a hada-hadar kuɗi na New York a 2021.