You are here: HomeAfricaBBC2023 05 04Article 1761041

BBC Hausa of Thursday, 4 May 2023

Source: BBC

Ana ci gaba da luguden wuta a birnin Khartoum

Hoton alama Hoton alama

Duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a Sudan, an ci gaba da samun hare-hare ta sama a Khartoum, babban birnin ƙasar.

Sojin ƙasar sun ce suna kai hare-hare a birnin ne domin koran dakaru masu adawa na Rapid Support Forces (RSF).

Faɗa na ci gaba da ƙanzacewa duk da alwashin da ɓangarorin biyu suka sha na tsawaita tsagaita wuta da ƙarin kwana uku.

Rahotanni ne cewa sama da mutun 500 ne aka kashe a rikicin, yayin da babu tabbas kan ainihin yawan mutanen da rikicin ya hallaka.

Babban hafsan sojin ƙasa na ƙasar, Janar Abdel Fattah al-Burhan da shugaban dakarun RSF, Janar Mohammed Hamdan Dagalo, wanda aka fi sani da Hemedti na ƙoƙarin yin kane-kane – inda ra’ayi ya sha banban kan yadda za a haɗe mayaƙan RSF a cikin dakarun ƙasar.

Manyan sojojin biyu sun amince da yarjejeniyar tsagaita wuta domin bayar da damar shigar da kayan agaji bayan tattaunawar diflomasiyya tsakanin ƙasashe masu maƙwaftaka, da Amurka da Birtaniya da kuma Majalisar Dinkin Duniya.