You are here: HomeAfricaBBC2023 06 26Article 1793048

BBC Hausa of Monday, 26 June 2023

Source: BBC

Ana caccakar Obama a Indiya kan kalamansa na kare haƙƙin Musulmai

Barack Obama, former US President Barack Obama, former US President

Shugabannin jam'iyya mai mulki a Indiya sun soki kalaman tsohon Shugaban Amurka Barack Obama game da take haƙƙin Musulmai a ƙasar.

Mista Obama ya faɗa a wata hira a makon da ya gabata cewa Indiya ka iya "fara ɓalɓalcewa" idan har ba ta kare haƙƙin marasa rinjaye.

Yana amsa tambaya ne game da yadda Shugaban Amurka Joe Biden ya kamata ya yi mu'amala da ƙasashe "'yan dimokuraɗiyya amma masu tsaurin ra'ayi".

Firaministan Indiya Narendra Modi na ziyarar aiki a Amurka a daidai lokacin.

Yayin ziyarar tasa, an yi masa maraba a Fadar White House cikin shagali, da liyafar abincin dare da kuma saka hannu kan wasu yarjejeniyoyi.

Kazalika Modi ya yi wa taron haɗin-gwiwar majalisun Amurka jawabi.

Kafofin yaɗa labarai a Indiya sun yaɗa hirar da Obama ya yi da wakiliyar CNN Christian Amanpour, wadda aka saki kafin ya gudanar da jawabi a majalisar.

Ta tambayi Obama: "Ta yaya shugaban ƙasa ya kamata ya yi mu'amala da shugabanni wajen ambaton sunansu ko kuma hulɗa da su?"

Mista Obama ya ce "abu ne mai sarƙaƙiya", kafin ya bayyana irin halin da ya shiga wajen hulɗa da ƙawayen Amurka da "ba sa bin salon dimokuraɗiyya da ya dace" amma kuma dole ƙasar ta ci gaba da ƙawance da su saboda wasu dalilai.

Ya ƙara da cewa "zai yi kyau" shugaban Amurka, idan zai yiwu, ya ƙalubalanci "lamurran da ba su dace ba" a bayyane ko a ɓoye.