You are here: HomeAfricaBBC2023 07 05Article 1798568

BBC Hausa of Wednesday, 5 July 2023

Source: BBC

Ana bincike don yadda gano aka yi hodar iblis ta shiga fadar White House

Fadar shugaban Amurka ta White House Fadar shugaban Amurka ta White House

Jami'an leƙen asirin Amurka na gudanar da bincike bayan gano hodar iblis a fadar shugaban Amurka ta White House cikin daren Lahadi.

Gano hodar a sashen da ake kira West Wing, da ya ƙunshi ofishin shugaban ƙasa da kuma sauran ofisoshin mataimakan shugaban ƙasa da ma'aikatansa, ya sanya fitar da jami'ai daga cikin ginin na wani ɗan lokaci.

Jami'an leƙen asiri sun gano hodar da ake zargi ne a wani wuri da rukunin masu yawon buɗe ido ke zuwa, a lokacin da suke binciken da suka saba na al'ada a fadar.

Shugaba Joe Biden da iyalinsa suna wata ziyara a Camp David, gidan da shugaban Amurka yakan je don hutawa a jihar Maryland, lokacin da abin ya faru.

Wani babban jami'in hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ya faɗa wa tashar CBS abokiyar ƙawancen BBC a Amurka cewa an gano abin ne a wani wurin ajiyar kaya wanda ma'aikatan fadar da kuma baƙi suka saba ajiye wayoyinsu na salula.

An rufe ginin fadar White House ɗin a matsayin riga-kafi da misalin ƙarfe 1:45 agogon Najeriya cikin daren Lahadi bayan gano hodar iblis ɗin.

Gwajin farko-farko da aka yi wanda jaridar Washington Post ta fara ba da rahoto, ya tabbatar cewa daga bisani hodar iblis ce.

Jami'an leƙen asiri za su jagoranci wani shirin yin cikakkiyar bita don gano yadda hodar iblis ɗin ta shiga fadar shugaban ƙasan Amurka, kamar yadda jami'ai suka faɗa wa CBS.

Sun ce za a yi nazarin kyamarori da litattafan tattara bayanan shigi da fice don tantance waɗanda suke da damar shiga yankin da aka samu hodar.

Hodar iblis ta kokyain na cikin rukuni na II na miyagun ƙwayoyi a Dokar Hana Ta'ammali da Ƙwaya, abin da ke nufin tana da matuƙar yiwuwar a yi amfani da ita a matsayin kayan maye, a cewar Hukumar Hana Ta'ammali da ƙwaya ta Amurka.

Sashen da ake kira West Wing wato Ɓangaren Yamma yana da girma a fadar White House, kuma yana da sassa masu yawa da ya ƙunshi ofisoshin shugaban ƙasa ciki har da Oval Office da kuma cibiyar bibiyar al'amura ko Situation Room.

Sashen kuma yana ƙunshe da ofisoshin mataimakiyar shugaban ƙasa da na shugaban ma'aikatan fadar White House da na sakataren yaɗa labarai da kuma sauran ɗaururwan ma'aikata da suke shiga.