You are here: HomeAfricaBBC2023 08 01Article 1816586

BBC Hausa of Tuesday, 1 August 2023

Source: BBC

An yi wa uwar da ta kashe 'ya'yanta ɗaurin rai da rai a Amurka

An samu Lori Vallow Daybell, mai shekara 50, da aikata babban laifin kisan kai An samu Lori Vallow Daybell, mai shekara 50, da aikata babban laifin kisan kai

An yanke wa wata uwa mazauniyar jihar Idaho ta Amurka da ke cikin wata ƙungiyar asiri ta masu hasashen aukuwar bala'i, hukuncin ɗaurin rai da rai a gidan yari bayan an same ta da laifin kashe 'ya'yanta masu tasowa biyu tare da haɗa baki wajen kashe kishiyarta.

An samu Lori Vallow Daybell, mai shekara 50, da aikata babban laifin kisan kai da tuhume-tuhume haɗa baki don aikata laifi a watan Mayu.

Lori Vallow ta kashe ɗanta Joshua wanda ake yi wa laƙabi da "JJ" Vallow, ɗan shekara bakwai da 'yarta Tylee Ryan 'yar shekara 16.

An gano gawawwakinsu ne binne a cikin gidan mijinta Chad Daybell a shekara ta 2020.

A ranar Litinin, Mai shari'a Steven Boyce ya yanke wa Lori Vallow hukuncin ɗaurin rai da rai har sau uku, ba tare da yiwuwar samun sakin je-ka-mu-ga-hankalinka ba.

"Kisan kai mafi munin da ba za a iya kwatantawa ba shi ne wanda uwa za ta halaka 'ya'yan cikinta, kuma shi ne haƙiƙanin abin da kika aikata," Mai shari'a Boyce ya ce.

Kotu ta saurari bayanan shaidu masu ratsa zuciya daga dangin mijinta a lokacin yanke hukuncin.

"Tylee da JJ sun kawo ɗumbin haske a wannan duniya," Colby Ryan, wani babban yayansu ya faɗa a cikin wani jawabi da masu shigar da ƙara suka karanta.

"Ina son a riƙa tunawa da su kamar yadda Allah ya halicce su amma ba a matsayin wani abin kallo ko abin buga labarinsu a jaridun duniya ba."

Mijinta, Chad Daybell shi man an tuhume kan mutuwar 'ya'yan da kuma mutuwar tsohuwar matarsa, Tammy Daybell, makonni kafin ya auri Lori Vallow. An tsara gudanar da shari'arsa a cikin shekara mai zuwa.

Chad Daybell marubuci ne da ya wallafa litattafan tashin duniya bisa koyarwar addinin Mormon.