You are here: HomeAfricaBBC2023 08 22Article 1829834

BBC Hausa of Tuesday, 22 August 2023

Source: BBC

An tuhumi Diezani Alison-Madueke kan zargin cin hanci a kotun Birtaniya

Diezani Alison-Madueke Diezani Alison-Madueke

Hukumar yaƙi da manyan laifuka a Birtaniya ta tuhumi tsohuwar ministar man fetur ta Najeriya a kotu, kan laifukan cin hanci.

Ana zargin Diezani Alison-Madueke da karɓar cin hancin miliyoyi barkatai na fam ɗin Ingila daga kwangilolin man fetur da iskar gas, da ta bayar don samun cin hanci.

Wata sanarwa da sashen yaƙi da cin hanci da rashawa na duniya a Hukumar Yaƙi da Manyan Laifuka ta Ƙasa ta ce ana zargin Diezani ta ci gajiyar aƙalla fam 100,000 kuɗi hannu, da samun zungura-zunguran motocin alfarma da tafiye-tafiyen jirgin sama na shata, da tafiya hutun alfama da kuma kadarori birjik a London.

Shugaban sashen yaƙi da cin hanci na ƙasashen duniya, Andy Kelly ya ce, "waɗannan tuhume-tuhume, muhimmin abu ne na wani cikakken bincike da sarƙaƙiya a cikin ƙasashen duniya."

Diezani Alison-Madueke, 'yar shekara 63, ta kasance a matsayin Shugabar Ƙungiyar ƙasashe Masu Arziƙin Man Fetur (OPEC), kuma ministar man fetur ta Najeriya a tsakanin 2010 zuwa 2015.