BBC Hausa of Friday, 28 April 2023

Source: BBC

An tilasta wa 'ya'yanmu bayar da fasfo ɗinsu kan a kai su Masar - Iyayen ɗaliban Sudan

Hausawa kan ce tsuguno bai ƙare ba, kan lamarin ɗaliban Najeriya da ke karatu a Sudan waɗanda gwamnatin Najeriyar ta ce za ta kwaso su.

Yayin da ake kukan cewa har yanzu akwai tarin ɗalibai a ƙasa - a gefe ɗaya kuma iyayensu na kukan lokacin na ƙurewa na yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma.

Iyayen ɗaliban da dama da BBC ta tattauna da su, sun yanzu haka halin da yaransu ke ciki ya fi wanda suka baro a Khartoum firgici.

Asma'u Yarima Muhammad ita ce sakatariyar Ƙungiyar Iyayen Daliban Najeriya da ke karatu a Sudan, ta ce yanzu haka 'ya'yanta biyu "na cikin tsakiyar sahara ba tare da sanin inda suka dosa ba".

A wajen iyayen da aka kwaso 'ya'yansu daga Khartoum, sun tsinci kansu cikin abin da masu iya magana ke cewa 'ana maganin ƙaba, kai na ƙara kumbura' domin kuwa wasu na jin inama ba a kwaso yaran nasu ba an kai su tsakiyar sahara a yasar.

Asma'u Yarima na da yara biyu masu shekaru 18, wato 'yan tagwaye ne duka maza.

Daya na karantar fannin zane, sai kuma ɗayan da ke karantar bangaren koyon aikin likita.

Tace yawancin ko wanne dare sukan yi waya da yaranta irin ta iyaye da 'ya'ya wadda rabinta nishaɗi ne, ɗaya rabin maganar karatu.

Amma tun daga 15 ga watan Afrilun da muke ciki rayuwa ta sauya, ta zama ƙunci ya yi mata dabaibayi.

Tace "kasa da awa biyu da muke magana da kai na yi magana da su, kuma suna shaidan cewa motoci 7 cikin 13 da suka taso daga Khartoum sun tsaya a sahara, suna neman a basu kuɗin aikinsu.

"Ganin cewa yaran ba su da kuɗin da za su ba su, sai suka ce to su bayar da fasfo ɗinsu sai su ƙarasa da su Aswan da ke cikin Masar, kamar yadda suka cimma yarjejeniya da gwamnatin Najeriya, in ji Hajiya Asamau.

Wata mahaifiya da BBC ta tattauna da ita da ta nemi a sakaya sunanta, tace sai da yarinyarta ta shiga mota cikin motocin da aka kawo amma daga baya aka fitar da ita.

"Kimanin sa'a biyu suka kwashe cikin motar, duk murna ta ishemu ni da yan uwanta muna ganin ta tsira, amma daga baya aka fitar da ita.

"Ta ce mutanen gari ne suka riƙa biyan daloli ana ɗaukarsu ana barin ɗaliban da aka aika motacin su kwaso.

Yarjejeniya da ke tsakin gwamnati da masu kwaso ɗalibai

Asma'u Yarima Muhammad ta ce yarjejeniyar da aka cimma tsakanin gwamnatin Najeriya da kamfanin jigilar motocin da zai kwashi ɗaliban Najeriya shi ne za a biya su dalar Amurka miliyan1.2.

"Gwamnati ta bai wa kamfanin dalar 400,000, saura dubu 800,000. Akan wannan sauran kuɗin ne suka tsayar da yaranmu a tsakiyar sahara suka ce sai an cika musu kuɗinsu.

"Kuma kuɗin nan garinsu aka yi magana za a biya ba wai a aika musu ta asusunsu na banki ba,'' in ji ta.

Sai dai Hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya ta ce daga safiyar yau Juma'a ne za a fara kwaso ɗaliban.

Kuma jirgin saman Air Peace da zai yi aikin kwashe ɗaliban da sauran 'yan Najeriya, zai tashi da ƙarfe 6 na yamma zuwa Aswan, cewar shugaban hukumar ba da agajin gaggawar.

Mustapha Habib Ahmed ya ce tuni motoci guda biyu ɗauke da ɗaliban da aka kwaso daga Khartoum suka isa bakin iyakar Masar.

Ya amsa cewa ba shakka sun samu matsala da wasu direbobi da suka zubar da ɗalibai a cikin Sahara kusa da Dongola, wani wuri mai nisan kilomita 411 daga Khartoum.

Mustapha Habib ya ce suna aikin shirya takardu tare da ofishin jakadancin Najeriya a Masar don ganin jirgin Air Peace ya samu damar jigilar 'yan Najeriyan daga birnin Aswan.

Ya ce tuni suka daidaita da kamfanin sufurin da ya zubar da ɗalibai a Sahara, har ma sun shiga motocinsu guda bakwai sun ci gaba da tafiya.