You are here: HomeAfricaBBC2023 08 21Article 1829099

BBC Hausa of Monday, 21 August 2023

Source: BBC

An soki shugaban hukumar kwallon kafar Sifaniya kan sumbatar 'yar wasa

An soki shugaban hukumar kwallon kafar Sifaniya, Luis Rubiales kan sumbatar Jenni Hermoso An soki shugaban hukumar kwallon kafar Sifaniya, Luis Rubiales kan sumbatar Jenni Hermoso

An soki shugaban hukumar kwallon kafar Sifaniya, Luis Rubiales kan sumbatar Jenni Hermoso a lebe, bayan Sifaniya ta lashe kofin duniya na mata.

Rubiales ya sumbaci Hermoso, yayin bikin karban kofi bayan wasan da Sifaniya ta doke Ingila da ci 1-0 a wasan karshe na ranar Lahadi.

"Ban ji dadi ba," in ji Hermoso a shafinta na Instagram, amma wata sanarwa da aka fitar daga baya a madadinta ta kare Rubiales''.

Ministar gwamnati Irene Montero ta bayyana lamarin a matsayin wani nau'i ne na cin zarafin mata da ake gudarwa a kullum.

Montero ta kara da cewa abu ne da a kan yi a boye kuma wani abu ne da bai kamata a mai da shi abin da ya dace ba.

A cikin kalaman da hukumar kwallon kafar Spain ta bayyana daga baya, Hermoso - wadda ita ce tafi kowa zura kwallaye a raga a Sifaniya - ta ce abin da ya faru ba wani abu ba ne illa nuni ne na soyayya.

Ta kara da cewa an sumbace ne, saboda farin cikin lashe gasar da kasar ta yi.

Rubiales ya shaida wa mai watsa shirye-shiryen Spain COPE cewa "sumba ce tsakanin abokai biyu da ke murnar wani abu" kuma wadanda suka yi wa abin wani fasara na daban a matsayin "marasa hankali".