You are here: HomeAfricaBBC2023 07 01Article 1795931

BBC Hausa of Saturday, 1 July 2023

Source: BBC

An shiga rana ta huɗu da mummunar tarzoma a Faransa

Tutar Faransa Tutar Faransa

Ma’aikatar kula da harkokin cikin gida ta Faransa ta ce an dan samu saukin tarzomar da ta barke a kasar ta nuna damuwa kan kisan da wani dansanda ya yi wa wani matashi mai shekara 17, a cikin mota, yayin da aka shiga rana ta hudu a rikicin, idan aka kwatanta da ranar Juma'a.

Ministan cikin gidan Gérald Darmanin ya ce a daren da ya gabata an kama mutum 471, idan aka kwatanta da na ranar Juma'a kusan 900.

Duk da kalaman da ministan cikin gidan ya yi na cewa an samu sassaucin tarzomar idan aka kwatanta da ranar Juma'a, an samu karin tashin hankalin a birane da dama na kasar ta Faransa.

Musamman ma birni na biyu mafi girma wato Marseille, inda hukuma ta ce an kama mutum kusan 90 daga masu tarzomar ta nuna bacin rai ga kisan da dan sanda ya yi wa matashi Nahel M, mai shekara 17, dan asalin Algeria, a birnin Nanter ta hanyar harbi, dab-dab a cikin mota, a ranar Talata.

Hotunan bidiyo da ke yawo na nuna irin mummunar barnar da aka yi a birnin na Marseille, inda aka samu barna mafi muni a tarzomar a daren da ya gabata.

A hotunan ana iya ganin yadda masu fushin suke artabu da ‘yan sanda, suna jefa wa jami’an wuta, da Cinna wuta a kan tituna da motoci da duk wani abu da za su iya barnatawa na hukuma.

An tura karin ‘yan sanda birnin bayan da magajin garin, Benoit Payan ya bukaci hakan.

An samu wata fashewa a tsohuwar tasahra jirgin ruwa ta birnin, inda hukumomi suka ce ana binciken me ya faru, amma bas a ganin fashewar ta hallaka ko jikkata wani

Kazalika an yada wani hoton bidoiyo da ke nuna yadda aka wawashe wani kantin sayar da kaya na Aldi, daga baya kuma aka Cinna wa kanti wuta.

Kafin wannan ma masu tarzomar su daka wawa a wani shagon sayar da bindiga a birnin na Marseille, said ai ‘ayn sanda sun ce mutanen sun debi bindigogin farauta ne, kuma ba harsasai.

Jumulla a fadin kasar na baza ‘yan sanda 45,000 a biranen da ake fama da rikicin, domin su kwantar da lamarin, inda rahotanni ke cewa na kama mutane kusan 500.

Gwamnatin kasar ta yi kira ga hukumomin yankuna da su dakatar da zirga-zirgar motocin bas da jirgin kasa na dare a fadin kasar baki daya, domin hana ci gaba da bazuwar tarzomar da kona Ababan sufurin.

Duk da haka wannan, tarzoma da ta bazu har zuwa Belgium mai makwabtaka da Faransar inda bayanai ke nuna cewa ana kama mutum dari daya a babban birnin kasar Brussels.

Can a birnin Liege ma rahotanni na cewa an kama mutuane kusan 30

Can a garin da tarzomar ta samo asali, Nanterre, tarzomar na kara kazancewa inda hatta ‘yan jarida ma kusan ke gamuwa da fushin jama’ar muddin suka ganka da kayan aiki.

Ana iya ganin yadda jama’a ke zagin ‘yan sanda da gaya musu maganganu.

Kyaftin din tawagar kwallon kafar kasar, Kylian Mbappe ya yi kira ga jama’a su yi hakuri tare da kwantar da hanakali yana mai cewa tashin hankali ba ya maganin komai, ya bukaci jama’a da su nuna alhini da neman tattaunawa da kuma sake gina kasar maimakon tarzomar.