You are here: HomeAfricaBBC2023 04 12Article 1747925

BBC Hausa of Wednesday, 12 April 2023

Source: BBC

An sayar da takalmin Michael Jordan kan $2.2 million

Takalmin da Michael da anka sayar kan $2.2 million Takalmin da Michael da anka sayar kan $2.2 million

An sayar da takalmin da Michael Jordan ya saka a gasar kwallon kwallon Amurka ta NBA kan $2.2 million.

An yi gwanjon takalmin da ake kira sneakers ranar Talata kamar yadda kamfanin gwanjon Sotheby ya sanar.

Zakakurin dan wasan ya saka takalmin da ake kira Air Jordan a wasa na biyu a 1998 karawar karshe da ya lashe kofi na shida na NBA.

Wannan cinikin da aka yi a yanar gizo ya dora Jordan a matakin farko da aka sayi kayan dan wasa mafi tsada a duniya.

Ya zarce yawan kudin takalminsa da aka sayar a watan Satumbar 2021 kan $1.5 million.

A bara aka sayar da wata rigar da ya yi amfani da ita a wasan kwallon kwando kan $10.1 million, kudin da aka biya mafi tsada ga kayan dan wasa a lokacin da aka yi gwanjon.

Jordan ya saka takalmin a zagaye na biyu a wasan da Chicago Bulls ta yi nasarar cin Utah Jazz 93-88. ranar 5 ga watan Yunin 1998.

Jordan ya ci wa Bulls maki 37 a fafatawar.

Kudin da aka sayi takalmin ya haura hasashen da kamfanin gwanjon Sotheby ya yi na $2 million, amma bai kai $4 million da aka ce za a iya samu ba.

Kamfanin gwanjon ya ce Jordan da kansa ya saka hannu wato signature a kan takalmin, sannan ya bai wa wani yaro kyauta mai dauko kwallo idan ya fita daga fili.

Sai dai Sotheby bai fayyace wanda ya mallaki takalmin ba mai lamba 13, bai kuma sanar da wanda ya saya ba.

Takalmin ya yi farin jini ga masu bibiyar kwallon kwandon Amurka mai launin baki da ja, wanda ya dunga sakawa a kakar da yake lashe kofin NBA.

Jordan, wanda yanzu yake da shekara 60 da haihuwa ya yi wasa a Bulls, kungiyar da ya lashe kofin NBA shida, sannan ya yi ritaya.

Daga baya ya koma buga kwallon kwandon Amurka a 2001, wanda ya yi kaka biyu a Washington Wizards.