You are here: HomeAfricaBBC2023 07 07Article 1799495

BBC Hausa of Friday, 7 July 2023

Source: BBC

An sanya wa dokar wariyar launin fata sunan ɗan Real Madrid Vinicius Jr.

Vinicius Jnr (saka) Vinicius Jnr (saka)

Gwamnatin Rio de Janeiro ta sanya wa dokar nuna wariyar launin fata sunan ɗan wasan REal Madrid Vinicius Jr.

Duka masu ruwa da tsaki na gwamnatin sun amince da sunan dokar 'Vini Jr law' da aka samar a watan Yuni, wadda za ta riƙa dakatar da duk wanda ya karya ta.

A kakar da ta wuce, ɗan wasa Vinicius mai shekara 22 ya fuskanci wariyar launin fata a wurare da dama.

"Yau wata rana ce ta musamman ina kuma fatan 'yan uwana za su yi alfahari da ni," kamar yadda ya bayyana a yayin bikin dokar da aka yi a filin wasa na Maracana, inda ya fara buga kwallonsa a matsayi babba a Flamengo.

"Ina da ƙarancin shekaru kuma ban taɓa tsammanin zan fuskanci wannan lamarin ba."

Rahotanni sun ce an ƙirƙiri dokar ne saboda cin zarafin da aka yi wa Vinicius a wasan da ya buga da Valencia a watan Mayu, wanda har sai da ya tsaya da wasan ya riƙa nuna waɗanda suka yi ma shi abin.

Dokar ta haɗa da yadda za a riƙa shigar da ƙorafi kan wariyar launin fata da kuma gangamin wayar da kan mutane game da matsalar.

An girmama Vinicius yayin taron da kyauta sannan an sanya hoton zanen ƙafarsa a filin cikin jerin masu ɗaukaka irin su Pele da Ronaldo da Garrincha.

A baya-bayan nan ya buga wasa da Senegal da Guinea, a wani mataki na wayar da kai game da wannan matsala.

Dan wasan da ya koma Madrid daga Flamengo a 2018 ya ce sau da yawa sai ya riƙa tunanin cewa bai dace a yi masa haka ba,