You are here: HomeAfricaBBC2021 03 17Article 1206766

BBC Hausa of Wednesday, 17 March 2021

Source: BBC

An sallami mijin Sarauniyar Ingila daga asibiti bayan kwashe wata guda

Mijin Sarauniyar Ingila ya bar asibiti da ke tsakiyar birnin London Mijin Sarauniyar Ingila ya bar asibiti da ke tsakiyar birnin London

Mijin Sarauniyar Ingila ya bar asibiti da ke tsakiyar birnin London bayan an yi nasarar yi masa tiyata a zuciyarsa.

An kwantar da Yarima Philip, mai shekara 99, a asibitin King Edward VII's da ke yankin Marylebone ranar 16 ga watan Fabrairu sakamakon rashin lafiyar da yake fama da ita.

An yi nasarar yi masa tiyata a bangaren zuciyarsa a wani asibitin London - St Bartholomew's.

Yariman ya koma fadar Windsor Castle bayan ya kwashe kwana 28, wanda shi ne lokaci mafi tsawo da ya taba kwashewa a asibiti.

Da farko ba a bayyana dalilin kwantar da shi a asibiti ba, sai dai a lokacin fadar Buckingham Palace ta ce rashin lafiyar tasa ba ta da alaka da cutar korona.

Yarima Philip da Sarauniyar Ingila, mai shekara 94, sun kwashe tsawon kullun da aka yi na baya bayan nan kan cutar korona a Ingila inda suka zauna a fadar Windsor Castle tare da ma'aikatansu marasa yawa wadanda ake yi wa lakabi da HMS Bubble.

Ma'auratan, wadanda suka kwashe shekara 73 tare, an yi musu allurar riga-kafin Covid-19 karon farko a watan Janairu.

Lokacin da yake jinya a asibitin King Edward VII's, dansa Prince of Wales.