You are here: HomeAfricaBBC2023 05 04Article 1760816

BBC Hausa of Thursday, 4 May 2023

Source: BBC

An saka sunan Ferdinand cikin gwarzayen Premier League

Tsohon dan wasan West Ham, Leeds United da Manchester United, Rio Ferdinand Tsohon dan wasan West Ham, Leeds United da Manchester United, Rio Ferdinand

An saka sunan tsohon dan wasan West Ham da Leeds United da Manchester United, Rio Ferdinand cikin gwarzayen Premier League.

Ferdinand, mai shekara 44 ya koma Manchester United daga Leeds a matakin wanda aka saya mafi tsada a Burtaniya a 2002, wanda ya lashe Premier League sida a kaka 12 a kungiyar Old Trafford.

Ya kuma dauki Champions League da Club World Cup karkashin Sir Alex Ferguson a United.

Haka kuma Ferdinand ya buga wa tawagar Ingila wasa 81, wanda ya fara taka mata tamaula yana da shekara 19 da haihuwa.

Ferdinand ya fara zama kwararre dan kwallo karkashin Harry Redknapp a West Ham, wanda ya yi shekara 20 a sana'ar taka leda.

Ya fara wasa yana da shekara 17 da haihuwa, wanda ya je wasannin aro a Bournemouth, ya fara yi wa Ingila tamaula a karawa da Kamaru a 1997.

Ya koma Leeds kan £18m a 2000, shekara biyu tsakani ya koma buga tamaula a Manchester United kan £29.1m a matakin wanda aka saya mafi tsada a Burtaniya kuma mai tsaron baya da aka saya mafi tsoka.

United ta bar Ferdinand ya koma QPR a 2014, wadda ta fadi daga gasar Premier League, shi kuma ya yi ritaya a watan Mayun 2015.