You are here: HomeAfricaBBC2023 08 14Article 1824818

BBC Hausa of Monday, 14 August 2023

Source: BBC

An raba maki tsakanin Chelsea da Liverpool a Premier

Hoto daga wasan Chelsea da Liverpool Hoto daga wasan Chelsea da Liverpool

Chelsea da Liverpool sun tashi 1-1 a wasan makon farko a gasar Premier League da suka buga ranar Lahadi a Stamford Bridge.

A minti na 18 da fara tamaula Liverpool ta ci kwallo ta hannun Luis Diaz, yayin da sabon dan wasan da Chelsea ta dauka a bana Axel Disasi ya farke a minti na 37.

Kan hutu Ben Chilwell ya ci wa Chelsea kwallo amma VAR ta ce ya yi satar gida, tun farko Liverpool ta zura kwallo a raga ta hannun Mohamed Salah amma VAR ta ce da satar gida.

Ranar Asabar 19 ga watan Agusta, Liverpool za ta karbi bakuncin Bournemouth a wasan mako na biyu a gasar Premier League ta bana.

Ranar Asabar 12 ga watn Agusta Bournemouth ta tashi 1-1 a wasan makon farko a babbar gasar tamaula ta Ingila ta kakar nan.

Ita kuwa Chelsea za ta je West Ham United ranar Lahadi 20 ga watan Agusta, domin buga karawar mako na biyu da za su kece raini a London Olympic Stadium.

Chelsea ta kare a mataki na 12 a teburin gasar Premier League a bara, yayin da Liverpool, wadda za ta buga Europa League a kakar nan ta kare a mataki na biyar.