You are here: HomeAfricaBBC2023 12 07Article 1894586

BBC Hausa of Thursday, 7 December 2023

Source: BBC

An nuna wa BBC hujjojin yadda mayaƙan Hamas suka yi wa matan Isra'ila fyaɗe

BBC ta gani kuma ta ji shaidun da ke nuna cewa an aikata fyaɗe a ciki Isra'ila BBC ta gani kuma ta ji shaidun da ke nuna cewa an aikata fyaɗe a ciki Isra'ila

BBC ta gani kuma ta ji shaidun da ke nuna cewa an aikata fyaɗe, da tashin hankali, da kuma lalata mata yayin harin da aka kai Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoba.

GARGAƊI: WANNAN MAƘALA NA ƊAUKE DA BAYANAI GAME DA FYAƊE DA KUMA LALATA DA ZA SU IYA TAYAR MUKU DA HANKALI

Mutane da da dama da ke aikin tattara shaidu kan gawarwakin mutanen da aka kashe sun faɗa wa BBC cewa sun ga shaidu daban-daban masu yawa da ke nuna cin zarafi ta hanyar lalata, ciki har da karya kwankwaso, da raunika, da yanka, kuma mutanen sun ƙunshi yara zuwa matasa da kuma tsofaffi 'yan fansho.

Wani bidiyo da wani shaida yake magana kan harin da aka kai kan bikin Nova, wanda 'yan sandan Isra'ila suka nuna wa 'yan jarida, ya bayyana fyaɗen taron-dangi, da kacaccala gawa, da kuma yi wa wani kisan gilla.

Bidiyon da Hamas ta ɗauka da kanta a ranar harin, da kuma hotunan da gawarwaki da aka samu bayan harin, sun nuna cewa maharan sun ci zarafin mata.

Ana ganin cewa waɗanda abin ya shafa 'yan ƙalilan ne suka tsira don bayar da labarin abin da ya faru.

'Yan sanda sun nuna wa 'yan jarida bayanin wata shaida mai ban-tsoro, wadda take wurin bikin na Nova yayin harin.

Ta bayyana yadda ta ga mayaƙan Hamas na yi wa wata mace fyaɗen taron-dangi kuma suka wulaƙanta ta kafin daga baya wasu suka harbe ta a ka.

A bidiyon, matar da aka kira da Shaida S, ta nuna a aikace yadda maharan suka dinga miƙa wa junansu matar don su yi mata fyaɗe.

"Tana nan da ranta," a cewar shaidar. "Tana ta zubar jini daga bayanta."

"Sun yanke nononta kuma suka wulla shi kan titi," in ji ta.

Ta ce daga baya an miƙa matar ga wani mutum sanye da kakin soja.

"Ya sadu da ita, sannan ya harbe ta a ka kafin ya gama. Bai ma saka wandonsa ba, kawai ya harbe ta kuma ya yi inzali."

Wani mutum da BBC ta yi magana da shi ya ce ya jiyo "ihun mutane a wurin bikin ana kashe su, da fyaɗe, da yanke kawunansu".

Da muka tambaye shi ta yadda aka yi ya tabbatar - ba tare da ya gani da idonsa ba - cewa ihun da ya ji na nufin a yi musu fyaɗe ba wai wani abu dabaan ba, ya ce ya tabbatar cewa abin da ya ji ba zai wuce fyaɗe.

"An yi wa wasu matan fyaɗe kafin a kashe su, an yi wa wasu bayan an raunata su, wasu kuma sun mutu lokacin da maharan suka yi musu fyaɗen," a cewar bayanan da ya yi. "Na yi bakin ƙoƙarina don na taimaka, amma babu abin da zan iya yi."

'Yan sanda sun ce suna da "bayanan shaidu masu yawa" na cin zarafi, amma ba su ba da wani ƙarin bayani ba game da yawansu. Da muka tuntuɓe su, har yanzu ba su yi magana da wani da aka ci zarafi ba wanda ya tsira.

Ministar Mata ta ta Isra'ila May Golan ta faɗa wa BBC cewa 'yan ƙalilan ne suka tsira daga cin zarafi da fyaɗen da aka yi musu, kuma ana ba su kulawa a asibitin ƙwaƙwalwa yanzu haka.

"Amma 'ya kaɗan ne sosai. An kashe mafi yawansu," in ji ta. "Ba za su iya magana ba - ko da ni, ko da gwamnati, ko kuma 'yan jarida."

Cikin bidiyon da Hamas ta ɗauka har da na wata mace da aka ɗaure hannayenta kuma aka yi garkuwa da ita ɗauke da rauni a hannunta da kuma jini a jikin wandonta.

A wasu kuma, an ga yadda aka tafi da wasu matan kusan tsirara, ko kuma ma tsirarar.

Hotuna da yawa aka gani daga wurin harin sun nuna wasu matan tsirara daa ƙugu zuwa ƙasa, ko kuma an karkatar da kamgensu zuwa ɓangare ɗaya, ƙafafuwa wawware, da kuma alamun damuwa a matancinsu.

"Da alama Hamas ta koyi yadda za ta yi amfani da fyaɗe a matsayin makamin yaƙi daga ƙungiyar ISIS a Iraƙi, da kuma abubuwan da suka faru a Bosnia," a cewar Dr Cochav Elkayam-Levy, wani ƙararre kan shari'a a cibiyar Davis Institute of International Relations ta Jami'ar Hebew.

"Na yi magana da 'yan mata uku waɗanda ke jinya a asibiti game da yanayin tunaninsu saboda fyaɗen da suka gani da idonsu," Minista May Golan ya faɗa mana.

"Sun ga fyaɗen ne bayan sun yi kamar sun mutu, kuma sun ji komai. Amma kuma sun rasa yadda za su yi da abin da suka gani."

Shugaban 'yan sandan Isra'ial, Yaacov Shabtai, ya ce da yawa daga cikin waɗnda ska kuɓuta sun kasa yin magana kuma yana ganin wasu daga cikinsu ba za su taɓa ba da shaidar abin da suka gani ba.

"An kwantar da samari da 'yan mata 18 a asibitin kula da lafiyar ƙwaƙwalwa saboda sun daina rayuwa yadda ya dace," in ji shi.

An ce wasu kuma sun fara tunanin kashe kansu. Wani da ke aiki da tawagar ya faɗa wa BBC cewa wasu daga cikinsu tuni suka kashe kan su.

An samu hujjojin ne mafi yawansu daga 'yan sa-kai da aka tura wurin bayan kai harin, da kuma waɗanda suka yi aikin gyara gawarwakin bayan sun isa barikin Shura na sojoji.

Ɗaya daga cikin 'yan sa-kai ɗin mai aiki da ƙungiyar addini ta Zaka ya bayyana min alamun azabtarwa da kuma wulaƙanci, waɗanda ska haɗa da, a cewarsa, mata masu ciki da aka farka cikinsu kafin a kashe ta, da kuma caka wa ɗan-tayinta wuƙa a cikinta.

BBC ba ta iya tabbatar da sahihancin wannan iƙirari ba, kuma su ma kafofin yaɗa labaran Isra'ila sun nuna shakku kan wasu hujjojin da masu sa-kai suka bayar game da harin na Hamas.

Wani mai suna Nachman Dyksztejna ya ba da bayanan ganin gawarwakin mata biyu a rukunin gidaje na Be'eri da aka ɗaure hannayensu da kuma ƙafafauwa a jikin gado.

"An ci zarafin ɗaya ta hanyar lalata kuma aka caka mata wuƙa a gabanta, tare da karairaya gaɓɓanta," a cewar bayanan da ya bayar.

A wurin bikin, ya ce "an cika wani wuri da gawarwaki na mata. An yaga rigunansu ta sama, amma kuma ƙasansu tsirara suke. Tsibi-tsibin gawarwaki. [...] Idan ka dubi kawunansu da kyau, za ku ga yadda aka harbe su da harsahi sau ɗaya a jikin kowacce."

An gano gawarwaki ɗaruruwa daga wurin da aka kai harin.

"A kwana biyar ɗin farko, har lokacin akwai 'yan ta'adda a cikin Isra'ila," kamar yadda May Golan ta bayyana. "Kuma akwai ɗaruruwan gawarwaki a ko'ina. An ƙona su ba tare da wasu gaɓoɓinsu ba, duk an lalata su."

"Wannan lamari da ya ƙunshi mutane da yawa," kamar yadda mai magana da yawun 'yan sanda Dean Elsdunne ya faɗa wa 'yan jarida.

Ma'aikatan barikin Shura ne, bayan an akawo gawarwakin, suka bai wa masu bincike hujjoji masu muhimmanci.

Lokacin da muka kai ziyara, ana ta ƙoƙarin fayyace gawarwaki.

Tawagogin da ke aiki a wurin sun faɗa mana cewa sun ga hujjojin fyaɗe da lalata a jikin mutanen da ake kawowa, ciki har da waɗanda aka karya wa kwankwaso saboda tsananin lalata.

"Mun ga mata asu shekaru daban-daban," ɗaya daga cikin sojojin, Kyaftin Maayan, ta faɗa wa BBC. "Mun ga waɗanda aka yi wa fyaɗe. Mun ga matan da aka tashi hankalinsu. Mun ga raunika, mun ga yanka da karaya, kuma mun lura cewa an ci mutuncinsu da lalata."

Na tambaye ta wace gawa ce ta nuna irin waɗannan alamu.

"Da yawa," in ji ta. "Mata masu yawa da 'yan mata."

Abu ne mawuyaci a iya tantance yawan mutanen da aka kashe, saboda yanayin da suke ciki.

"Ai dole ma suna da yawa," a cewar wata sojan da ta nemi mu bayyana sunanta na farko kawai, Avigayil. "Da wuya a iya fadar adadin. Na yi aiki kan wasu gawarwakin da aka ƙona kuma ban sani irin halin da suka shiga ba. Gawarwakin da kuma ba su da ɓangare na ƙasa a jikinsu - su ma ban sani ba ko fyaɗe aka yi musu. Amma dai matan da aka yi wa fyaɗe ƙarara? Akwai su da yawa. Sun wuce iyaka ma."

Wani zubin wasu da ke aiki kan gawarwakin kan ce "gommai" ne, amma sukan ce har yanzu ana tattara hujjoji.

Kwamatin da Dr Elkayam-Levy ke jagoranta wajen tatara hujjojin fyaɗe, na kira ga al'ummar duniya ta amince cewa abin da ya faru ranar 7 ga watan Oktoba tsari ne na musaman don cin zarafi, wanda ke matsayin laifukan cin zarafin ɗan'adam.

"Mun ga alamu na zahiri," in ji ta. "Saboda haka ba tsautsayi ba ne, ba gama-gari ba ne. Sun zo ne da umarni na musaman. Fyaɗe ne [...] a matsayin kisan ƙare-dangi."

David Katz na sashen binciken laifukan intanet, wanda ke cikin masu binciken, ya faɗa wa 'yan jarida cewa ya yi wuri a tabbatar da cewa an tsara fyaɗe da lalata ne a matsayin ɓangare na yaƙin, amma kuma bayaan da aka samu daga wayoyin mayaƙan Hamas zuwa yanzu sun nuna "an tsara komai da komai".

"Za mu yi sakaci idan muka ce mun iya gano hujja tun yanzu [...] amma kuma duk abubuwan da aka aikata a wurin an yi su ne a tsare," in ji shi. "Babu wani tsautsayi a ciki. An tsara fyaɗen nan."

Gwamnatin Isra'ila ta nuna wani kundi da ta ce an samu daga mayaƙan na Hamas da ke nuna goyon bayan cewa a tsara aikata lalatar ne. Ta fitar da bidiyon yadda ake bincikar wasua daga cikin mayaƙan, inda suka amince cewa an kai wa mata hari da gangan.

A makon da ya wuce, sashen karehaƙƙin mata na MDD ya fitar da sanarwa cewa "ta yi tir da harin da Hamas ta kai" kuma "ta kaɗu da bayan shaidun da ke bayyana cin zarafin jinsi da kuma lalata a lokacin harin".

Dr Elkayam-Levy ta faɗa kafin sanarwar ta MDD cewa sashen ya ɗauki lokaci bai ce komai ba.

"Wannan ce aika-aika da aka fi samun hujja a rayuwar ɗan'adam," kamar yadda ta faɗa min.

"Isra'ila ta sauya tun daga washegarin 7 ga watan Oktoba," in ji shugaban 'yan sanda Yaacov Shabtai.

Yayin da ake tsaka da jimamin abin da ya faru da matan, Kyaftin Maayan da ke cikin majalisar Shura ta tantance mutanen, ta ce lokacin da ta fi shiga damuwa shi ne "lokacin da ta ga burushin gyaran gashin ido, da yarin da suka saka a wannan ranar".

Na tambaye ta me ta ji ta ga hakan a matsayinta na mace.

"Ta'addanci," a amsarta. "Ya kiɗima mu."