You are here: HomeAfricaBBC2023 01 13Article 1694618

BBC Hausa of Friday, 13 January 2023

Source: BBC

An nada jami’in da zai binciki yadda Shugaba Biden ya mallaki takardun sirri na gwamnatin Amurka

Shugaban Amurka Joe Biden Shugaban Amurka Joe Biden

Babban mai shigar da kara na gwamnatin Amurka Merrick Garland ya nada wani jami’I na musamman domin ya binciki Shugaban Amurka Joe Biden kan badakkalar wasu takardun sirri mallakin gwamnati da aka gano a ofisoshinsa.

Robert Hur wanda tsohon babban jami’in ma’aikatar shari’a ne a karkashin gwamnatin tsohon Shugaba Donald Trump, shi ne zai jagoranci binciken.

A makonnin da suka gabata, na gano wasu takardun gwamnatin Amurka na sirri cikin wani ofishin da Shugaba Biden yayi amfani da shi bayan ya sauka daga mukamin mataimakin shugaban kasa a gwamnatin Barack Obama.

Fadar White House ta sanar cewa za ta hada kai sosai da mai binciken.

Gano wadannan takardun ya kasance wani abin kunya ga Mista Biden, ganin cewa ba a jima ba da tsohon shugaba Trump ma ya fuskanci irin wannan binciken.

 Ranar 2 ga watan Nuwambar bara aka gano takardu na farko a wata cibiya mai suna Penn Biden Center, wadda mallakin Shugaba Biden ce da ya kaddamar a birnin Washington DC. An dai mika dukkan takardun ga gidan adana takardu na gwamnatin kasar, wato National Archives, kamar yadda Mista Biden ya sanar da kansa.

Mista Garland ya ce an kuma gano wasu takardun na daban ranar 20 ga watan Disamba a gidan Shugaban Amurkar da ke Wilmington na Jihar Delaware, kuma ya kara da cewa a safiyar Alhamis da ta gabata, lauyoyin Mista Biden sun kira masu bincike domin sanar da su cewa an gano karin wata takardar ta sirri a wani gidan Mista Biden din.

Bayan wani kwarya-kwaryan bincike ne da babban lauyan gwamnati John Lausch ya gabatar, Mista Garland ya ga ya dace a nada mai bincike na musamman domin ya bincike yadda Shugaba Biden ya mallaki wadannan takardun sirrin. 

Yayin wata ganawa da yayi da manema labarai da safiyar Alhamis, Mista Biden ya sake nanata maganar da yayi cewa lauyoyinsa sun sanar da jami’na ma’aikatar shari’a dukkan abubuwan da suka gano, kuma ya dauki batun da muhimmanci sosai.