You are here: HomeAfricaBBC2023 07 29Article 1814738

BBC Hausa of Saturday, 29 July 2023

Source: BBC

An kori da Juventus daga buga Europa Conference na bana

Yan wasan Juventus Yan wasan Juventus

Hukumar kwallon kafar Turai, Uefa ta kori Juventus daga buga Europa Conference League na kakar 2023/24.

Hakan ya biyo bayan samun kungiyar da laifin karya dokar ciniki daidai samu da ake kira 'Financial Fair Play'(FFP).

Haka kuma hukumar ta ci tarar Chelsea da karya dokar ta FFP, biyan da ta mika sakamakon hada-hadar kudinta, wanda ba a ta kammala ba.

Hukumar ta ce lamarin ya shafi kasuwancin da ta yi tsakanin 2012 da kuma 2019.

An ci tarar Juventus fam miliyan 17.14, ita kuwa Chelsea za ta biya fam miliyan 8.57.

Kungiyar Italiyan za ta biya rabin tarar da aka yi mata, idan har nan da kaka uku za ta bi dokar ta kashe kudi daidai samu.

Ita kuwa Chelsea ta amince za ta biya dukkan kudin tarar da aka gindaya mata.

Chelsea ta kashe fam miliyan 600, wajen sayen 'yan wasa 19, tun bayan da Todd Boehly ya karbi jan ragamar kungiyar a Mayun 2022.

Sai dai an samu kungiyar Stamford Bridge da karya ka'idar hukumar a cinikin 'yan wasa bakwai a lokacin Roman Abramovich.

'Yanzu an bai wa hukumar kwallon kafar Italiya ta sanar da wadda za ta maye gurbin Juventus a gasa mai daraja ta uku ta cin kofin zakarun Turai.

Watakila Fiorentina ce, wadda ta yi rashin nasara a hannun West Ham a karawar karshe Conference Legue, wadda ita ce ta yi ta takwas a teburin Serie A da ya wuce.

An tuhumi Juventus, bayan da kungiyar ta amince da biyan hukumar kwallon kafar Italiya tarar fam 620,000 kan abin da ya shafi biyan albashin 'yan wasa.

A kakar da ta wuce an kwashe wa Juventus maki 10 a gasar Serie A.

Juventus ta ce ba za ta daukaka kara ba, za ta biya tarar da aka gindaya mata, sannan za ta bi dokar ta kashe kudi daidai samu kamar yadda aka kafa ta.