You are here: HomeAfricaBBC2023 09 21Article 1848650

BBC Hausa of Thursday, 21 September 2023

Source: BBC

An kori babban sakataren hukumar ƙwallon Sifaniya

Yan wasan Sifaniya Yan wasan Sifaniya

Hukumar Ƙwallon Ƙafar Sifaniya ta kori babban sakatarenta Andreu Camps tare da neman afuwa kan abin da ya faru bayan wasan ƙarshe na cin Kofin Duniya na mata.

Hukumar ta ce ta hanzarta yi wa tsarinta garambawul domin cika alƙawarin da ta yi wa 'yan wasa.

Tun da farko, mafi yawan 'yan wasan sun amince da su kawo ƙarshen kaurace wa tawagar ƙasar.

'Yan wasan sun fara ƙaurace wa tawagar ne bayan tsohon shugaban hukumar Luis Rubiales ya sumbaci 'yar wasa Jenni Hermoso lokacin nasarar da Sifaniya ta samu a kan Ingila a wasan ƙarshe na cin kofin duniya na mata a ranar 20 ga watan Agusta.

Bayan kawo ƙarshen ƙauracewar nasu a ranar Laraba, hukumar ta ce ta sallami Camps daga aiki.

Har ila yau, ta nemi afuwar 'yan wasan musamman Hermoso don a cewar hukumar an sanya ta cikin wani yanayin da ba son ran ta ba ne.