You are here: HomeAfricaBBC2023 03 27Article 1738778

BBC Hausa of Monday, 27 March 2023

Source: BBC

An kashe yara a harin da matashiya ta kai kan wata makaranta a Amurka

Police officers for di crime scene Police officers for di crime scene

An kashe ƙananan yara uku a wani harin da ake zargin wata matashiya ta kai kan wata makaranta mai suna Covenant School da ke yankin Nashville.

'Yan sandan Nashville sun ce an gano wadda ta kai harin kuma matashiya ce 'yar shekara 28.

Haka zalika sun ce harin ya yi sanadin "jikkata mutane da dama".

Shugaban Amurka Joe Biden ya gabatar da jawabi a kan harbe-harben na Nashville.

"Abin takaici ne," Biden ya ce game da mummunan hari. Ya bayyana lamarin a matsayin wani "baƙin mafarkin iyali mafi muni".

"Sai mun ƙara dagewa don kawo ƙarshen tashe-tashen hankulan bindiga," in ji Biden. "Abu ne da ke kassara al'ummominmu, kuma yana durƙusar da ruhin wannan ƙasa."

Don haka, Biden ya ce "Ina sake kira ga Majalisar Wakilai ta zartar da dokata ta haramta bindigogin zuwa yaƙi". "Lokaci ya yi".

An kai harin ne kan makarantar kuɗi ta mabiya addinin Kirista, inda ɗalibai kimanin 200 kama daga 'yan shekara 11 zuwa 12 suke karatu.

Jami'ai ba su tabbatar da shekarun waɗanda aka kashe a harin ba.

'Yan sanda sun ce sun tunkari mai kai harin, kuma a yanzu har ma ta mutu.