You are here: HomeAfricaBBC2023 05 11Article 1765205

BBC Hausa of Thursday, 11 May 2023

Source: BBC

An kama wasu mata a Kano kan zargin satar yara da neman miliyoyi na fansa

Hoton alama Hoton alama

'Yan sanda sun ce sun kama wasu mata guda biyu, cikin mutanen da ake zargi da satar ƙananan yara tare da neman miliyoyin kuɗi a matsayin fansa daga iyayensu a Kano.

Cikin matan har da wata, mai shekara 45, wadda suke zargin tana cikin gungun mutum huɗu da suka sace wani yaro, tare da neman kuɗin fansa fiye da naira miliyan biyar.

Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ta zargi matar wadda gwaggon yaron ce, da shirya maƙarƙashiyar sace Almustapha Bashir a farkon watan jiya.

Ya ce tun da farko, mutanen da suka saci yaron ɗan shekara shida ranar 4 ga watan Afrilu sun nemi mahaifinsa ɗan unguwar Ƙofar Ruwa a tsakiyar birnin Kano ya biya naira miliyan ashirin kafin su saki yaron.

Daga bisani in ji sanarwar Abdullahi Kiyawa, mahaifin da masu garkuwa da yaron sun daidaita, a kan naira miliyan biyar da dubu ɗari da hamsin.

"Bayan gudanar da bncike, an kuɓutar da yaron ba tare da ko rauni ba, tare da kama babbar wadda ake zargi da shiryawa da kuma tsara yadda za a sace Almustapha" sanarwar ta ce.

Haka kuma 'yan sanda sun kama duk waɗanda ake zargi da hannu a satar yaron, waɗanda matasa ne 'yan shekara 24 zuwa 27 daga unguwar Sheka.

A wani al'amarin daban kuma, rundunar 'yan sandan ta ce ta kama wata bazawara 'yar shekara 25, kan zargin sace 'yar tsohon mijinta mai suna Hafsat Kabiru tare da neman kuɗin fansa, naira miliyan uku.

Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce a ranar 8 ga watan Mayu ne wani Kabiru Shehu Sharaɗa a tsakiyar birnin Kano ya kai rahoton cewa tsohuwar matarsa ta sanar da shi cewa 'yarsu ta ɓata, kuma wasu mutane sun kira ta wayar salula inda suka nemi sai an biya naira miliyan uku kafin a sako ta.

Ya ce bayan gudanar da bincike ne aka kuɓutar da yarinyar a ƙaramar hukumar Madobi tare da kama da mahaifiyar yarinyar.

Mai magana da yawun 'yan sandan ya yi iƙirarin cewa mahaifiyar yarinyar ta amsa da bakinta cewa ita ce ta ɗauki 'yar tata kuma ta kai ta maɓoya, sannan ta nemi babanta ya biya kuɗin fansar.

Sanarwar Abdullahi Haruna Kiyawa ta ce 'yan sanda suna ci gaba da bincike.