You are here: HomeAfricaBBC2023 08 17Article 1826933

BBC Hausa of Thursday, 17 August 2023

Source: BBC

An gayyaci Yarima Bn Salman zuwa Birtaniya, cewar majiyar gwamnati

Yariman Saudiyya mai jiran gado, Mohammed Bn Salman Yariman Saudiyya mai jiran gado, Mohammed Bn Salman

An gayyaci yariman Saudiyya mai jiran gado, Mohammed Bn Salman zuwa Birtaniya, a cewar wata majiyar gwamnati.

Fadar firaministan Birtaniya ta Gini mai Lamba 10 ta ce za su ba da tabbaci a kan tattaunawar da zai yi da firaminista ta hanyar da aka saba.

Sai dai wata majiyar gwamnati daban ta ce babu dalilin da zai sa a yi tunanin cewa ziyarar ba za ta yiwuwa.

Idan ta tabbata, ita ce ziyara ta farko tun bayan kisan gillar da aka yi wa an jarida Jamal Khashoggi a ofishin jakadancin Saudiyya da ke birnin Istanbul a 2018.

Jaridun Financial Times da the Times ne suka fara bayar da rahoton wannan ziyara ta Yarima Bn Salman.

Ƙasashen Yamma sun yi tofin Allah-tsine a kan kisan gillar da aka yi wa Jamal Khashoggi, mai sukar gwamnatin Saudiyya a lokacin.

Ministocin Birtaniya sun ce an aikata kisan ne ta hanyar "ƙeta mai tayar da hankali" inda daga bisa suka sanya takunkumi a kan 'yan Saudiyya 20 da ke da hannu a kisan.

Hukumomin leƙen asirin Amurka sun ƙarƙare da cewa yariman jazaman shi ne ya ba da izinin aikata kisan, duk da yake ya musanta duk wani hannu a ciki.

An kuma faɗa wa BBC cewa Saudiyya tuni ta fara shirye-shirye kan wannan ziyara aƙalla tsawon wata ɗaya da ya wuce.

Mai yiwuwa ne ziyarar za ta gudana a cikin watan Oktoba, ko da yake zuwa yanzu ba a sa rana ba.

'Yan jam'iyyar Liberal sun soki lamirin wannan ziyara, inda suka ce ziyarar tana aika wata manuniya cewa yarima mai jiran gadon "na iya ci gaba da yin gatsalinsa kuma mu da abokan ƙawancenmu, ba za mu yi komai ba".

Mai magana da yawun harkokin waje ta jam'iyyar Layla Morgan na cewa: "abu ne da ya shallake hankali a ce Rishi Sunak ya shimfiɗa dardumar karɓar Mohammed bin Salman.

"Wannan mutumin - wanda ya ba da izinin aikata kisan ƙeta ga Jamal Khashoggi kuma ya jagoranci tarihin kare 'yancin ɗan'adam na ƙasƙanci - bai kamata ya samu kyakkyawar karɓa daga gwamnatin Birtaniya ba."