You are here: HomeAfricaBBC2023 07 04Article 1797863

BBC Hausa of Tuesday, 4 July 2023

Source: BBC

An ga hamshaƙin watan da ya haske sassan duniya a daren Litinin

Hoton alama Hoton alama

Mutane sun yi ta ɗaga kai sama cikin al'ajabi lokacin wata ya bayyana cikin haske da girman da aka saba gani ranar Litinin da daddare.

A cewar hukumar binciken sararin samaniyan Amurka ta NASA, ana ganin hamshaƙin watan da ke bayyana a cikin Yuli da cikarsa har tsawon sama da kwana uku.

Watan kan yiwo ƙasa-ƙasa fiye da yadda aka saba gani a kan hanyar da yake zagaye Duniyar Az.

Hakan na faruwa ne saboda hanyar da watan yake bi, ba cikakken zagaye yake yi ba a dalilin maganaɗisun janyo abu ƙasa da Duniyar Az ke yi.