You are here: HomeAfricaBBC2023 09 30Article 1853978

BBC Hausa of Saturday, 30 September 2023

Source: BBC

An fitar da Andy Murray daga gasar China Open

Andy Murray Andy Murray

Tauraron ɗan ƙwallon Tennis na Birtaniya, Andy Murray, ya sha kashi a wasan wasan da ya buga da Alex de Minaur a gasar China Open.

Tsohon mai lamba ta 1 a duniya, Murray ya sha kashi da ci 6-3 5-7 6-6 (8-6) a wasan da suka kara a birnin Beijing.

Murray ne fara jagorantarwasan a turmi na uku da 5-2, inda ya samu maki biyu kan kura-kuran De Minaur, kafin ɗan ƙasar Australiyan ya farfaɗo.

Murray ya sake rasa wani makin ana daf da tafiya hutu kuma daga nan De Minaur ya miƙe.

Karo na biyar ke nan da mai shekara 36 ɗin ke yin nasara a hannun De Minaur, wanda ke matsayi na 12 a duniya.

Yanzu De Minaur zai kara da Tommy Paul ko kuma Daniil Medvedev a zagaye na biyu.

Ɗan wasan mai shekara 24 ya zama mutum na huɗu da ya doke Murray a wasa biyar a jere bayan Rafael Nadal, da Roger Federer, da Novak Djokovic.

Rashin nasarar da ya yi a ranar Alhamis na nufin karo uku ke nan De Minaur na fitar da Murray daga wata gasa a wannan shekarar.