You are here: HomeAfricaBBC2023 02 13Article 1713560

BBC Hausa of Monday, 13 February 2023

Source: BBC

An fallasa yadda cuwa-cuwar neman aiki ke yawaita a Indiya

Hoton alama Hoton alama

Da sanyin safiyar wata rana a watan Disamba, 'yan sanda a Gabashin Jihar Rajasthan suka ga wata motar bas ta nufi yankin birnin Udaipur, sai suka bi ta a baya.

A daren ranar, an kwarmata musu labarin za a fitar da tambayoyin jarabawar daukar malamai na makarantun gwamnatin jihar ta bayan fage kafin miliyoyin mutane su zauna domin rubuta jarabawar.

An sanya cibiyoyi 1,193 domin rubuta jarabawar, wadda aka dade ana tsimayi a ranar 24 da Disamban.

A kasar Indiya, inda ake rububin neman aikin gwamnati, labarin bin bayan fage wajen neman aikin ba sabon abu ba ne.

Wasu masu neman aikin sukan yi satar amsa, ciki har da sayan takardun jarabawar kafin ranar, ko kuma su biya a rubuta musu.

Motar bas din ta Udaipur, tana hanyarta ce ta zuwa cibiyar rubuta jarabawa, sai 'yan sanda suka yi zargin akwai yiwuwar a fitar da takardun tambayoyin jarabawar a hanyar.

Da farko sai suka tsaya a can baya lokacin da motar ke zagaya wani gida na wasu mintuna. Sai suka tsayar da ita.

"A ciki mun samu malaman makarantar gwamnati guda hudu suna rubuta wa masu neman aiki 20 jarabawa," kamar yadda wani jami'i da ya bukaci a sakaya sunansa ya bayyana wa BBC.

Ana zargin masu neman aikin sun biya malaman ne, wadanda aikinsu shi ne duba yadda jarabawar ke tafiya a cibiyar.

Kudi-duk da cewa 'yan sandan ba su bayyana nawa masu neman aikin suke biya ba, amma akalla masu neman aikin guda 20 ne suka biya aka rubuta musu jarabawar a madadinsu.

'Yan sanda sun yi zargin cewa wadanda ake zargin sun yi amfani da katin shaida na bogi.

An kama jimillar mutum 48 da suke da hannu a wannan harkalla a wannan safiyar, wanda hakan ya sa hukumomi a jihar suka soke jarabawar.

Har yanzu ba a samu damar kama manyan masu harkallar guda biyu daga cikin wadanda ake zargi ba, wanda hakan ya sa gwamnati ta sanya ladar Dala 1,500 (£1,245) a kan kowane daga cikinsu, kamar yadda Shugaban 'Yan sandan Udaipur, Vikas Sharma ha bayyana wa BBC.

lamarin yana cikin na kusa-kusan nan da suka faru a cikin jerin almundahanar da ke faruwa, inda ake samun takardun tambayoyin muhimman jarabawar gwamnati na fita ta bayan fage, ko kuma wasu su biya kudi a rubuta musu.

Tun a shekarar 2018, akalla an soke daukar aiki guda 12 a jihar bayan an fitar da takardun tambayoyin jarabawar kafin lokacin rubutawa- wasu lokutan ranaku kafin ranar jarabawar wasu lokutan kuma awanni ne kawai a tsakani.

Masu neman aiki da dama sun bayyana cewa sun fara gajiya da neman aiki duba da yanayin hanyoyin da ake bi wajen daukar ma'aikatan.

"Ba na tunanin zan sake zuwa gwajin neman aiki, " inji wata mai suna Santosh Kumawat, mai shekara 30 da ta taba zuwa rubuta jarabawar daukar aiki sau biyu daga Jihar Maharashtra da ke makwabtaka da Rajasthan.

"Na farko da na zo suka ce an dakatar da jarabawar. Na biyu kuma, har mun fara rubutawa, sai suka dakatar da mu, suka karbe takardun saboda an fitar da takardun tambayoyin jarabawar kafin mu fara," inji ta.

Matsalar ba a Rajasthan kawai ta tsaya ba- harkallar ta riga ta karade Indiya, kasancewar miliyoyin mutane ba su da aiki, kuma suna neman aikin ruwa a jallo.

Masanin Kimiyyar Siyasa, Pankaj Kumar, wanda shi ne Shugaban Hukumar Ma'aikata ta Uttar Predash ya ce ma'aikatan gwamnati ne suke nuna cewa, "akwai tagomashi sosai a aikin gwamnati, wanda hakan ya sa suke rububinsa.'

Aikin gwamnati a Indiya a lokuta da dama sai mutum ya mutu idan ya fara, wanda a cewar Mista Kumar miliyoyin mutane suna jira sai bayan wani lokaci su samu aiki, sannan " Kashe kudi ta bayan fage yanzu ya zama wata sunnar masu neman aikin. "

A Gujarat, garin Firaiminista Narendra Modi, akalla sau takwas ana soke daukar malaman makaranta da kananan akawu daga shekarar 2014 zuwa yanzu saboda fitar da takardun jarabawar.

A Kudancin Jihar West Bengal, dole hukomomi a jihar suka kafa kwamitin bincike a bara bayan an samu bullar takardun tambayoyin jarabawar daukar malamai a kafafen sadarwa awanni kadan kafin a fara rubuta jarabawar.

Haka labarin yake a jihohin Tsakiyar Jihar, kamar Jihar Madhya Pradesh, wadda aka samu harkallar almundahanar daukar ma'aikata a shekarar 2009, inda aka samu masu neman aikin jinya sun dauko wasu daga wasu jihohin domin su rubuta musu jarabawar.

Haka kuma an fitar da takardun tambayoyin jarabawar aka sayar wa masu neman aikin, kafin gwamnati ta gano, tare da kama dubban mutane.

Jihohin Bihar da Uttar ma sun yi kaurin suna a wannan harkalla.

A Bihar, a wasu lokutan ana hana dalibai shiga jarabawa da takalma da safa domin hana su satar amsa.

A da can, hukumomi sun samu tara da tsare iyayen daliban bisa zarginsu da taimakon 'ya'yansu, har ma kai wasu gidan yari.

A Jihar Uttar Predash, ana rubuta jarabawar ce tare da kulawar kyamarori

'Yan sanda sun ce ana samun matsala ne lokacin da ake kai takardun tambayoyin jarabawar zuwa cubiyoyin rubuta jarabawar.

A wasu lokutan, kamar a Udaipur har sauya suna da yanayi wasu suke yi, wanda hakan ya sa yake da wahalar gaske a kama su.

A yanzu dai babu wata doka kai tsaye da aka tanada domin wannan laifi, domin yawancin laifukan ana hada su ne cikin laifuka irinsu zamba da sata, wadanda duk ake bayar da belinsu.

Wasu jihohin kamar Uttarakhand sun yi dokar daurin rai da rai ga wadanda aka kama da laifin, amma wasu na ganin dokar ba ta hana komai ba.

Ashok Rathore, babban jami'i mai binciken fallasar jaridu a Rajasthan ya ce akwai bukatar hukumomi su yi dokokin da za su magance matsalar.

"Mun bukaci gwamnati ta sa 'yan sanda da kananan hukumomi tun kafin lokacin rubuta jarabawar ya zo, ta yadda za a tabbatar takardun tambayoyin ba su kai ga hannun masu satar amsar ba-kamar yadda ake tsare kuri'un zabe,' inji shi.

Amma wasu masana na ganin lamarin yana kara fito da matsalar rashin aikin yi da ya yi was Indiya katutu a fili ne, inda miliyoyin mutane suke neman aiki.

Raahin aikin yi a Indiya ya kai kashi 8 a Disamban bara, kamar yadda Cibiyar Bibiyar Tattalin Arzikin Indiya (CMIE) ta fitar. Amma bai kai kashi 7 ba a 2021.

Akalla mutum miliyan 20 ne suke aiki a Indiya a matakin Gwamnatin Tarayya da jihohi, sannan an ce akwai akalla gurabun aiki guda miliyan daya a yanzu haka.

"Shekara 30 bayan saukaka harkokin kasuwanci a Indiya, har yanzu kasar ba ta da ayyukan da za ta ba dimbin mutanenta da suka kusa kai biliyan 1.4," inji marubuci, kuma maj sharhi a kan harkokin siyasa, Gurchafan Das.

Ya kara da cewa aikin gwamnati abun sha'awa ne ga wasu, domin mafi yawan 'yan kasar aikin kansu suke yi, kuma ba sa wani cin moriyar gwamnati.

"Ba kamar aikin gwamnati ba, aikin kamfanoni ba su da fansho da tabbas," inji Mista Das.

Masu neman aikin sun ce cigaban rayuwarsu na fuskantar tasgaro kasancewar samun takardun tambayoyin jarabawa na maimaituwa, wanda hakan ya sa suke fargabar za su iya wuce shekarun neman aiki.

"Na je makarantar koyon koyarwa domin in samu aikin gwamnati, amma yawanci jarabawar da na je sai a soke," inji Devender Sharma.

Mai shekara 30 din, wanda dan birnin Bikaner na Jihar Rajasthan ne ya kwashe sama da shekara 10 yana neman aikin gwamnati a jihar.

"Iyayena suna zargin cewa ni ne nake fadi jarabawar, alhalin tsarin ne yake kayar da mu," inji shi.