You are here: HomeAfricaBBC2023 09 30Article 1853990

BBC Hausa of Saturday, 30 September 2023

Source: BBC

An cinye Inter Miami a wasan ƙarshe ba tare da Messi ba

Lionel Messi Lionel Messi

Lionel Messi da ke jinya ya kalli yadda ƙungiyarsa ta Inter Miami ta yi rashin nasara a hannun Houston Dynamo a wasan ƙarshe na US Open Cup da 2-1.

An cire Messi mai shekara 36 daga wasan da suka buga da Toronto FC a makon da ya gabata saboda "wani tsohon rauni", abin da ya sa bai buga wasansu da Orlondo City ba ke nan, wanda suka yi canjaras a ranar Litinin.

Bugun finareti da Griffin Dorsey da Amine Bassi suka ci ne ƙwallayen da Houston ta ci a wasan da aka buga a Fort Lauderdale da ke Florida.

Sai kuma Josef Martinez da ya farke wa Miami ƙwallo ɗaya a mintunan ƙarshe.

Golan Houston, Andrew Tarbell, ya bige ƙwallaye uku a wasan don taimaka wa ƙungiyar tasa ɗaukar kofin karo na biyu cikin shekara biyar.

Shi ma abokin wasan Messi, Jordi Alba, bai buga wasan ba saboda rauni.

Kocin Miami Gerardo Martino ya ce murmurewar Messi ce abin da suka saka a gaba yanzu.