You are here: HomeAfricaBBC2023 07 04Article 1797857

BBC Hausa of Tuesday, 4 July 2023

Source: BBC

An ci tarar Neymar dala miliyan uku a Brazil

Neymar Jnr Neymar Jnr

Hukumomin Brazil sun ce ɗan kwallon ƙafar ƙasar Neymar zai biya tarar reais miliyan 16 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 3.33 saboda saɓa dokar muhalli.

Dan wasan ya karya dokar ne lokacin da yake gida wani makeken gida a yankin kudu maso gabashin Brazil da ke gaɓar teku.

Aikin ƙasaitar ya saɓa ka'idar amfani da kuma kai-kawon tsaftacaccen ruwa, ƙasa da duwatsu, tun a ƙarshen watan jiya hukumomin yakin suka yi wannan ƙorafi amma sai a ranar Litinin ɗin nan aka tabbatar da tarar.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters kakakin ɗan wasan yaƙi cewa komai kan batun.

Gidan da yake ginawa yana tsakiyar garin Mangaratiba ne da ke kudancin gaɓar tekun Rio de Janeiro.

Hukumomin muhalli na garin Mangaratiba cikin wata sanarwa da suka fitar sun ce an karya dokar tsara muhalli yayi gina wani lafki a ƙasaitaccen gidansa."

Baya ga tarar, ofishin antoni janar na jihar zai ci gaba da bincike kan lamarin tare da yan sanda da masu lura da muhalli da sauransu.