You are here: HomeAfricaBBC2021 03 05Article 1196629

BBC Hausa of Friday, 5 March 2021

Source: BBC

An ci Liverpool wasa biyar a jere a Premier a karon farko a tarihi

Kocin Liverpool Jurgen Klopp Kocin Liverpool Jurgen Klopp

Chelsea ta yi nasara a kan Liverpool da ci 1-0 a wasan Premier League da suka kara a Anfield ranar Alhamis.

Kungiyar ta Stamford Bridge ta ci kwallon ta hannun Mason Mount saura minti uku su je hutun rabin lokaci.

Da wannan sakamakon Chelsea ta koma ta hudu a kan teburi da maki 47, ita kuwa Liverpool mai rike da kofin ta yi kasa zuwa ta bakwai da 43.

Wannan ce rashin nasara ta biyar a jere da aka doke Liverpool a Premier League a karon farko a tarihi.

Wasan farko da Liverpool ta ci a gida a kakar nan, shi ne ranar 16 ga watan Disamba da ta doke Tottenham 2-1.

Thomas Tuchel ya ja ragamar wasa 10 a Chelsea ba a doke shi ba a dukkan fafatawa, inda ya ci karawa bakwai da canjaras uku.

Wasa biyar da aka doke Liverpool a jere a Premier League:

Premier League 3 ga watan Fabrairu

    Liverpool 0 - 1 Brighton
Premier League 7 ga watan Fabrairu

    Liverpool 1 - 4 Manchester City
Premier League 13 ga watan Fabrairu

    Leicester 3 - 1 Liverpool
Premier League ranar 20 ga watan Fabrairu

    Liverpool 0 - 2 Everton
Premier League 4 ga watan Maris

    Liverpool 0-1 Chelsea