You are here: HomeAfricaBBC2023 02 07Article 1710026

BBC Hausa of Tuesday, 7 February 2023

Source: BBC

An ceto Atsu daga baraguzai bayan girgizar kasa a Turkiya

Christian Atsu Christian Atsu

An zakulo dan wasan tawagar Ghana, Christian Atsu daga cikin baraguzai a wani gini a Hatay.

Manajan dan wasan ne da ake kira Mustafa Özat ya sanar da gidan radiyo na Turkiya.

Dan wasan da ke taka leda a Hatayspor ya makale a buraguzan, bayan girgizar kasa da ta kashe mutum 4,800 a Turkiya da Syria ranar 6 ga watan Fabrairu.

Hatay birni ne da ke kusa da inda girzigar kasar ta yi barna mai yawa, harma gini ya danne daraktan wasannin kungiyar, Taner Savut, har yanzu ba labari.

Dan kwallon ya buga wasa 107 a Newcastle da Chelsea da Everton da kuma Bournemouth.

''An ceto Atse daga baraguzan da suka danne shi, ya kuma ji rauni,'' in ji Ozar kamar yadda ya sanar da gidan radiyon Turkiya na Radyo Gol.